Yaki da annobar covid-19 a Kano: Ganduje ya nemi tallafin biliyan N15 daga FG

Yaki da annobar covid-19 a Kano: Ganduje ya nemi tallafin biliyan N15 daga FG

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa ta nemi ta aika kokon barar neman tallafin biliyan goma sha biyar zuwa gwamnatin tarayya domin yakar annobar coronavirus.

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ne ya sanar da hakan yayin wata tattaunawa da shi a gidan talabijin na 'channels', kamar yadda jaridar Daily Trust ta wallafa da yammacin ranar Laraba.

A cewar gwamnan, har yanzu gwamnatinsa ba ta karbi ko ficika ba daga gwamnatin tarayya a matsayin tallafin yaki da annobar covid-19 da ta bulla a jihar ba.

A cikin sati guda da bullar annobar covid-19 a jihar Kano, cutar ta harbi kusan mutane 100.

A cikin makon jiya ne gwamna Ganduje ya kaddamar da dokar kulle Kano na tsawon sati biyu domin dakile yaduwar annobar covid-19 a cikin jiharsa.

Ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta yi amfani da biliyan N15 din wajen biyan ma'aikatan lafiya 'yan sa-kai da aka dauka aiki domin taimakawa ma'aikatan lafiya a cibiyar killacewa da cibiyar gwaji.

Yaki da annobar covid-19 a Kano: Ganduje ya nemi tallafin biliyan N15 daga FG
Gwamnan Kano; Dakta Abdullahi Umar Ganduje
Asali: Twitter

Kazalika, ya ce za a sayawa ma'aikatan kayan aiki tare da samar da karin cibiyoyin gudanar da gwajin kwayar cutar covid-19 a Kano.

"Kowa ya san cewa jihar Kano ta fi kowacce jiha a Najeriya yawan mutane, kowa ya san cewa cibiyar gwaji guda daya tak a AKTH ba za ta wadatar ba," a cewar Ganduje.

Kafin wadanan kalamai na gwamna Ganduje, Legit.ng ta wallafa cewa Sanata Barau Jibrin ya roki gwamnatin tarayya ta taimakawa jihar Kano da kudi domin ta shawo kan annobar cutar covid-19.

DUBA WANNAN: El-Rufa'i ya saka sabuwar doka a Kaduna bayan warkewarsa daga cutar covid-19

Sanata Jibrin, mamba mai wakiltar sanatoriyar Kano ta arewa a majalisar dattijai, ya bayyana hakan ne a cikin wani jawabi da ya fitar ranar Laraba a Abuja.

A cikin jawabin da ya fitar, wanda kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya wallafa, sanata Barau ya ce gwamnatin jihar Kano ta na bukatar kudi, kayan aiki da karin cibiyoyin gwaji.

A cewar dan majalisar, jihar Kano ta cancanta ta samu tallafi mai tsoka daga gwamnatin tarayya, saboda ita ce jiha mafi yawan jama'a Najeriya.

Sanata Jibrin ya bayyana cewa tallafawa Kano tamkar bawa arewacin Najeriya da ma kasa baki daya tallafi ne, saboda muhimmancin da jihar keda shi a kasa.

Dan majalisar ya roki shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya taimakawa gwamnatin Kano domin ta samu sukunin shawo kan annobar cutar covid-19 da ke yi wa jihar barazana a halin yanzu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel