Za a fara gwajin riga-kafin cutar korona a Jamus
Mahukuntan Lafiya a kasar Jamus sun bayar da lamunin fara gwajin rigakafin cutar Coronavirus, annobar da dugunzuma al'ummomi tare da hana ruwa gudu a duniya.
Jaridar NY Times ta ruwaito cewa, wani kamfanin hada magunguna na kasar, BioNTech, shi ne ya samar da rigakafin wadda za a fara gwajinta domin tabbatar da ingancinta.
BioNTech tare da hadin gwiwar babban kamfanin Amurka na hada magunguna, Pfizer, su ne suka samar da rigakafin wadda za a fara gwajinta kamar yadda mahukuntan lafiyar Jamus suka bayyana.
A matakin farko za a fara gwajin rigakafin ne kan mutane 200 masu cikakkiyar lafiya a Jamus, kana a mataki na biyu a gudanar da gwajin kan wadanda ke da hadarin kamuwa da cutar korona.
Jami'in cibiyar alluran rigakafi na kasar Jamus, Paul Ehrlich Institut shi ne ya bayar da shaidar hakan a ranar Laraba. Ya ce za a yi gwajin kan mutane 'yan tsakanin shekara 18 zuwa 55.
Za kuma a gudanar da gwajin rigakafin a Amurka da zarar an sami amincewar gwamnatin kasar.
Ministan lafiya na Jamus, Jens Spahn, ya ce wannan babbar alama ce da ke nuna ci gaba da aka samu na samar da rigakafi a kasar.
A makon da ya gabata ne gwamnatin kasar China ta amince da wasu alluran rigakafin coronavirus guda biyu domin gwaji a jikin mutane.
KARANTA KUMA: Zafafan hotuna 15 na Rahama Sadau da 'yan uwanta mata uku
Wani bangare na kamfanin Sinovac Biotech da kuma cibiyar nazarin kwayoyin halittu ta Wuhan, su ne suka kirkiri alluran biyu.
Haka kuma sakataren kiwon lafiya kasar Birtaniya, Matt Hancock, ya bayar da shaidar samuwar rigakafin cutar COVID-19 kuma ranar Alhamis za'a fara gwadawa kan masu cutar.
Masana ilmin kimiya na jami'ar Oxford ne suka kirkiri maganin rigakafin mai suna ''ChAdOx1 nCoV-19."
Da yake jawabi yayin taron da aka gudanar a fadar Firam Ministan Birtaniya, 10 Downing Street, Hancock ya ce gwamnatin na bakin kokarinta wajen ganin rigakafin cutar ta tabbata.
A halin yanzu dai ana ci gaba da gwajin rigakafin da aka samar a kasashen Amurka da China.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng