El-Rufai ya sha alwashin daukar mataki a kan masu barkowa cikin Kaduna
A karshen watan Maris ne gwamnatin jihar Kaduna a karkashin Malam Nasir El-Rufai ta bada umarnin cewa kowa ya zauna a gidansa, a yunkurin takaita yaduwar cutar COVID-19.
Idan ba ku manta ba, mataimakiyar gwamnan, Dr. Hadiza Balarabe ta bada wannan sanarwa. Gwamnatin jihar ta bada dama ga matafiya su bi babban titin da ya bulle ta bayan gari.
Kusan wata guda da bada wannan umarni, an gano ana saba wannan doka. Ana zargin dinbin mutane su kan shigo jihar Kaduna daga wasu wurare ba tare da an tabbatar da lafiyarsu ba.
Wani matashi mai suna Anas Jumare ya yi amfani da shafin sa na sada zumunta na Tuwita, ya sanar da gwamna Nasir El-Rufai abin da ke faruwa a daya daga cikin manyan titunan jihar.
Wannan Bawan Allah ya fadakar da gwamnan jihar Kaduna da kuma shugaban ma’aikatan fadar gwamnatinsa, Mohammed Sani Dattijo game da yadda wasu Baki daga waje ke shigowa jihar.
KU KARANTA: Gwamna El-Rufai ya warke, ya bukaci kowa ya nemi tsummar rufe fuska
“Wannan titin Nnamdi Azikwe ne, ta yankin unguwar Bakin-Ruwa, manyan motoci dauke da mutane su na shigowa cikin gari. Bisa dukkan alamu daga yankin Kudu su ka fito.” Inji sa.
Malam Jumare ya kara da fadakar da mai girma gwamnan cewa: “An dauki tsawon lokaci ana wannan a lokacin kulle.” Jumare ya nuna hotunan da za su tabbatar da abin da ya ke fada.
Bayan jin cewa mutane su na saba dokar da aka kafa a wannan lokaci da ya kamata ace mutane su na kulle a gidajensu, gwamna El-Rufai ya yi wuf ya maidawa wannan mutumi martani.
Malam El-Rufai ya ce: “Mun samu labarin wannan kuma mu za mu dauki matakin gaggawa da ya dace.” Gwamnan ya kuma kara da godewa wannan mai kishi da ya fadakar da hukuma.
“Nagode da ka zama mai kishi, Allah ya yi maka albarka, ya sa kowa ya zama irinka.” Duk da gwamnan ya na jinyar COVID-19 a lokacin, ya sanar da wasu kwamishinoninsa lamarin.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng