Ganduje ya sasauta dokar kulle a Kano

Ganduje ya sasauta dokar kulle a Kano

Gwamnatin Kano ta sassauta dokar kulle da ta saka a fadin jihar domin dakile yaduwar annobar cutar covid-19.

Mataimakin gwamnan jihar Kano, Dakta Nasiru Yusuf Gawuna, ne ya sanar da hakan yayin ganawarsa da manema labari a gidan gwamnatin Kano, kamar yadda 'Leadership' ta rawaito.

An sassauta dokar ne daga karfe 6:00 na safiyar ranar Juma'a zuwa karfe 12:00 na dare domin bawa jama'a damar yin shirin azumin watan ramadana.

Da ya ke magana amadadin gwamnan jihar Kano, Dakta Gawuna ya ce sassauta dokar ya zama dole domin bawa jama'ar jihar sukunin yin shirin azumin watan Ramadana da aka saba yi kowacce shekara.

Ya bayyana hakan ne yayin da ya ke jawabi ga manema labarai a kan dokar kulle da kuma zuwan watan azumi, watau watan 'Ramadan'.

Ya bayyana cewa gwamnatin jiha ta kara wa'adin rufe makarantun jihar har zuwa sanarwa ta gaba.

Ganduje ya sasauta dokar kulle a Kano
Dakta Nasir Yusuf Gawuna
Asali: Facebook

Ya ce gwamnati ta dauki wannan mataki ne bisa la'akari da kara yaduwar da annobar cutar covid-19 ke yi a jihar.

Kazalika, ya roki jama'ar Kano su cigaba da bawa gwamnati hadin kai a kokarinta na dakile yaduwar annobar covid-19 a jihar.

DUBA WANNAN: El-Rufa'i ya saka sabuwar doka a Kaduna bayan warkewarsa daga cutar covid-19

Kafin fitowar wannan sanarwa, Legit.ng ta wallafa cewa gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa a shirye ya ke ya bawa jama'ar jihar damar zuwa siyayyar azumin watan Ramadan.

Gwamnan ya ce: "Akwai yuwuwar mu bawa jama'a koda sa'o'i kadan ne don samun damar yin cefanen azumi saboda watan Ramadan da zai iya kamawa ranar Juma'a."

Gwamna Ganduje, wanda ya zanta da jaridar The Cable, ya bayyana cewa: "A kullum masu kamuwa da cutar covid-19 kara yawa su ke yi a jihar Kano. Don haka babu bukatar dage dokar hana zirga-zirgar a yanzu".

A daren Talata ne ma'aikatar lafiya ta jihar Kano ta tabbatar da cewa mutum 73 ne ke dauke da cutar Covid-19 a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel