Covid-19: Gwamnatin Kebbi ta saki fursunoni 111, ta ba kowannensu N10,000

Covid-19: Gwamnatin Kebbi ta saki fursunoni 111, ta ba kowannensu N10,000

- Gwamnatin jihar Kebbi ta fara rage cunkoson da ke gidajen gyaran halin jihar

- An fara rage mazauna gidajen gyaran halin a ranar Talata bayan amincewar gwamnan jihar

- Alkalin alkalan jihar, Mai shari'a Sulaiman Muhammad Ambursa ne ya fara sakin mazauna gidajen gyaran halin

Gwamnatin jihar Kebbi ta fara aikin rage cunkoso a gidajen gyaran hali na jihar. Hakan ya biyo bayan amincewar Gwamna Abubakar Atiku Bagudu don biyayya ga umarnin gwamnatin tarayya.

An fara rage yawan mazauna gidajen gyaran halin ne a ranar Talata inda aka fara da tattara sunayen mazauna gidan gyaran halin, kamar yadda jaridar Daily Trust ta bayyana.

Antoni Janar din jihar Kebbi kuma kwamishinan shari'a, Barsita Ramatu Adamu Augie, ta sanar da sakin mazauna gidan gyaran halin har dari da goma sha daya.

Alkalin alkalan jihar, Mai shari’a Sulaiman Muhammad Ambursa ne ya saki mazauna gidajen gyaran halin.

Kwamishinan ta kara da sanarwa da cewa gwamnatin jihar ta biya kudin da aka yankawa mazauna gidan gyaran halin tare da ba kowannensu N10,000 don mayar da kansu gidajensu.

Ta shawarci wadanda aka saki din da su zama masu halayya ta gari a kowanne lokaci ga al’umma da abokan zamansu.

Covid-19: Gwamnatin jihar ta saki mutum 111 daga gidan gyaran hali tare da hada musu da N10,000

Covid-19: Gwamnatin jihar ta saki mutum 111 daga gidan gyaran hali tare da hada musu da N10,000
Source: UGC

DUBA WANNAN: Kano: Ganduje ya yi magana a kan dage dokar hana zirga-zirga

A yayin jawabi, alkalin alkalan jihar, Mai shari’a Suleiman Muhammad ya ce wasu daga cikin mazauna gidan gyaran halin sun samu an sakesu ne sakamakon rangwamen fadar shugaban kasa.

Wasu daga ciki kuwa an sakesu ne bayan an bayar da belinsu.

Ya yi kira ga wadanda basu mora daga wannan rangwamen da su kasance masu hakuri da addu’a ko za su kasance masu rabo a nan gaba.

Za a ci gaba da rage mazauna gidajen gyaran halin da ke kananan hukumomin Yauri, Zuru, Jega da Bagudo na jihar.

A wani bangare, gwamnatin jihar ta musanta rahoton da ke yaduwa na cewa ta mayar da sansanin 'yan bautar kasa da ke Dakingari zuwa cibiyar killacewa.

"Wannan zance ne mara tushe ko makama. Ana yada shi ne don kokarin dakile kokarin gwamnatin jihar wajen hana yaduwar annobar coronavirus a jihar," takardar ta ce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel