Covid-19: Korona ta kashe mutum biyu a Borno da Ribas, mutum 6 sun sake kamuwa

Covid-19: Korona ta kashe mutum biyu a Borno da Ribas, mutum 6 sun sake kamuwa

- A ranar Laraba ne gwamnatin jihar Borno ta tabbatar da mutuwar mutum na biyu a jihar sakamakon annobar Covid-19

- Hakazalika, gwamnatin jihar Ribas ta tabbatar da cewa mutum na uku mai shekaru 61 ya harbu da muguwar cutar a jihar

- Gwamnatin jihar Borno ta bada umarnin rufe kasuwanni tare da yi musu feshi don wanda ya rasun dan kasuwa ne a Biu

A ranar Laraba ne gwamnatin jihar Borno ta sanar da mutuwar mutum na biyu sakamakon muguwar cutar coronavirus a jihar.

Mataimakin gwamnan jihar, Alhaji Umar Kadafur, wanda shine shugaban kwamitin yaki da yaduwar cutar a jihar, ya sanar da hakan a ranar Laraba yayin jawabi game da annobar a jihar.

"Mamaci dan asalin garin Biu ne kuma ya samu cutar bayan ya yi mu'amala da mai cutar ne.

"Daya daga cikin wadanda suka yi mu'amala da shi dan kasuwa ne a kasuwar Biu. Bayan aukuwar wannan lamarin, gwamnatin jihar ta bada umarnin rufewa tare da yi wa kasuwar feshi.

"A yau, an samu mutum 144 wadanda suka yi mu'amala da mai cutar, 55 daga ciki an gwada su kuma an samu 9 daga ciki dauke da cutar," yace.

Covid-19: Korona ta kashe mutum biyu a Borno da Ribas, mutum 6 sun sake kamuwa
Covid-19: Korona ta kashe mutum biyu a Borno da Ribas, mutum 6 sun sake kamuwa
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Kano: Ganduje ya yi magana a kan dage dokar hana zirga-zirga

Hakazalika, gwamnatin jihar Ribas ta samu mutum na 3 a jihar da ke dauke da muguwar cutar.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta wallafa, Wani manajan otal ne mai shekaru 61 wanda ya samu uban gidansa da ya dawo daga Abuja amma sai ya mutu bayan kwanaki kadan a cikin watan Fabrairu.

Kwamishinan lafiya na jihar, Farfesa Princewill Chike ya sanar da manema labarai ne a ranar Laraba.

Farfesa Chike ya ce an mika dan shekaru 61 zuwa cibiyar killacewa sannan ana ci gaba da binciko wadanda ya yi mu'amala da su.

A halin yanzu, manajan otal din ne mutum na uku da ya kamu da cutar. Ta farko a jihar matashiya ce mai shekaru 19 sai wani wanda ya yi murabus mai shekaru 62.

An kwashe masu dauke da cutar don samun taimakon masana kiwon lafiya a cibiyar killacewa ta Ogali-Eleme da ke jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel