Yanzu-yanzu: A karo na farko, an samu bullar Korona a Adamawa

Yanzu-yanzu: A karo na farko, an samu bullar Korona a Adamawa

Gwamna Ahamdu Fintiri na jihar Adamawa, a ranar Laraba ya tabbatar da mutum na farko da aka samu ya kamu da COVID-19 a jihar.

A wata sanarwa ta musamman da gwamnan ya fitar ya ce mutum na farko da aka samu da kwayar cutar yana daga cikin wadanda suka dawo daga jihar Kano ne kuma aka musu gwajin.

Ya yi bayanin cewa mutumin ya kai kansa asibiti bayan da ya dawo daga Kano kuma ya fara jin alamun rashin lafiya inda aka killace shi aka yi masa gwaji sannan aka gano ya kamu da cutar.

Yanzu-yanzu: Coronavirus ta shiga Adamawa

Yanzu-yanzu: Coronavirus ta shiga Adamawa
Source: Twitter

DUBA WANNAN: COVID-19: Gwamnatin Kano ta mayar da Almajirai 419 zuwa Katsina

"Sakamakon gwajin da ya fito a ranar Laraba ya nuna ya kamu da cutar," in ji gwamnan.

Ya kara da cewa gwamnati ta fara daukan matakai domin tallafawa majinyata da suke cibiyar killace masu cutar da ke Yola kuma an fara binciken gano wadanda suka yi muammala da shi.

Ya sanar da cewa akwai yiwuwar a saka dokar hana fita a jihar nan gaba domin dakile yaduwar annobar a jihar.

Gwamnan ya jadadda cewa bayan bullar cutar a kasar, gwamnatin Adamawa ta dauki dukkan matakan da suka dace kamar rufe iyakokin ta, takaita zirga zirga domin hana cutar shigowa jihar.

Kazalika, gwamnan ya ce jihar Adamawa tana da kwamitin kar ta kwana na COVID-19 da ke aiki dare da rana domin ganin an ci galaba a kan cutar yayin da tawagar masu saka idanu kan yaduwar cutar suma suna aikinsu yadda ya dace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel