Zafafan hotuna 15 na Rahama Sadau da 'yan uwanta mata uku

Zafafan hotuna 15 na Rahama Sadau da 'yan uwanta mata uku

- Jarumar Kannywood Rahama Sadau ta watsa wasu kayatattun hotunanta da na 'yan uwanta mata uku

- 'Yan uwan jarumar na da kyawun halitta tamkar yadda ita kanta ta kasance

- Kyawawan matan sun saba watsa zafafan hotunan kawunansu a shafukansu na dandalin sada zumunta

Daya daga cikin fitattun jaruman dandalin wasan kwaikwayo na Kannywood, Rahama Sadau, ta watsa wasu zafafan hotunanta tare da wasu 'yan uwanta mata uku.

Rahama Sadau na daya daga cikin tsala-tsalan jarumai wadanda suka fito daga yankin Arewacin Najeriya.

Baya ga tallata irin nishadi da jin dadin rayuwarta a zaurukan sada zumunta, jarumar kuma tana ci gaba da watsa wa duniya irin kyawun sura ta 'yan uwanta mata uku.

Jarumar tare da 'yan uwanta sun saba watsa hotunansu ne a dandalin sada zumunta da ake kira Instagaram, domin masoya da magoya su kashe kwarkwatar idanunsu.

'Yan uwan nata; Zainab, Ayeesha da kuma Fatima na da kyawun halitta tamkar wadda Mai Duka ya azurta jarumar da shi.

KARANTA KUMA: Jihohi 25 da aka samu bullar cutar Covid-19 a Najeriya - NCDC

Duk da cewa akwai bambancin sura da kuwa halittar jiki, amma akwai kamanceceniya ta jini da 'yan matan ke yi da junansu.

A cewar jarumar, tsananin goyon baya na hakika da ta ke samu daga bangaren 'yan uwan na ta, ya sanya ba za ta taba yin kasa a gwiwa ba wajen bayyanawa duniya irin muhimmancinsu a gare ta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel