Gwamnatin Nasarawa ta saki fursunoni 115, ta ba kowannen su N5,000

Gwamnatin Nasarawa ta saki fursunoni 115, ta ba kowannen su N5,000

- Gwamnatin jahar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, ya sallami fursunoni 115 daga cibiyoyin tsare masu laifi a jahar

- Gwamna Sule ya bukaci wadanda suka ci moriyar wannan shiri na afuwa da su samu abu mai amfani su yi domin bayar da gudunmawa wajen gina kasar

- Har ila yau gwamnan ya ba kowannensu N5,000 domin su yi kudin motar zuwa gidajensu

Gwamnan jahar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, ya sallami fursunoni 115 daga cibiyoyin tsare masu laifi a jahar.

Gwamna Sule, wanda ya samu wakilcin Atoni-Janar kuma kwamishinan shari'a na jahar, Dr. Abdulkarim A. Kana a taron sakin fursunonin, ya yi masu nasiha.

Ya kuma bukaci wadanda suka ci moriyar wannan shiri na afuwa da su samu abu mai amfani su yi domin bayar da gudunmawa wajen gina kasar.

Gwamnatin Nasarawa ta saki fursunoni 115, ta ba kowannen su N5,000
Gwamnatin Nasarawa ta saki fursunoni 115, ta ba kowannen su N5,000
Asali: Twitter

Dr. Kana ya mika wa wadanda suka amfana daga shirin afuwan N5,000 kwannen su, domin su yi kudin motar zuwa gidajen su.

A cewarsa: “Hakan na bisa tsarin umurnin shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma shirin afuwa da shugaban kasar ya yi wa fursunoni da dama a fadin kasar.

“Gwamnan jahar Nasarawa ya bukaci kowani mutum a cikinku da ya rungumi kyakyawar dabi'a, sannan ku yi amfani da darusan da kuka koya a lokacin da kuke a gidan gyaran hali wajen kawo ci gaba a kasar.

Ya kuma bukaci da su yi hankali da miyagun abokai da kuma hatsarin annobar COVID-19 wanda ake fama da shi a yanzu, ta hanyar bin sharudan da gwamnati ta gindaya.

KU KARANTA KUMA: Za mu yi amfani da lambar BVN don binciko talakawa masu bukatar tallafi - Minista

A ranar 9 ga watan Afrilu, shugaba Buhari ya yi umurnin sakin fursunoni 2,600 a fadin kasar, duk daga cikin kokarin da gwamnatinsa ke yi na rage cinkoso a gidajen yari da kuma hana yaduwar COVID-19 a Najeriya.

A wani labari na daban, mun ji cewa wani bidiyo na wasu mazauna jihar Kano ya jawo cece-kuce a kafafen sada zumuntar zamani.

A bidiyon, an ga matasan jihar na karya dokar nisantar juna da gwamnatin tarayya da ta jihar suka gindaya.

An ga samari cike da filin kwallo suna taka leda inda wasu daban ke zagaye dasu don kallon wasan.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel