Coronavirus: Magungunan gargajiya sun taimaka wajen warkar dani – Kakakin majalisar Edo Frank Okiye

Coronavirus: Magungunan gargajiya sun taimaka wajen warkar dani – Kakakin majalisar Edo Frank Okiye

Frank Okiye, kakakin majalisar dokokin jahar Edo, ya yi kira ga hadin gwiwa wajen yakar annobar coronavirus yayinda ya warke daga annobar bayan gwaji sau biyu yana nuna baya da cutar.

Legit.ng ta tuna cewa Okiye ya harbu da cutar wacce ta karade duniya, kuma mataimakin gwamnan jahar Edo, Philip Shaibu ne ya bayyana lafiyar kakakin majalisar ranar 25 ga watan Maris.

An tattaro cewa ya kamu da cutar ne a yayin ziyarar da ya kai kasar Ingila, sannan ya fara samun kulawar likitoci bayan ya fara nuna alamun cutar.

Coronavirus: Magungunan gargajiya sun taimaka wajen warkar dani – Kakakin majalisar Edo Frank Okiye

Coronavirus: Magungunan gargajiya sun taimaka wajen warkar dani – Kakakin majalisar Edo Frank Okiye
Source: Depositphotos

Okiye, ya yi godiya ga Gwamna Godwin Obaseki kan yadda yake tafiyar da lamarin annobar, inda ya bayyana cewa koda dai ba a samo maganin Covid-19 ba, “cutar ba tana nufin mutum zai mutu ba ne” kamar yadda mutane ke zato.

“Cutar ba mutuwa bace... Abune da aka sani cutar bata da magani. Ba tana nufin mutuwa bace. Mutane su bi umurnin gwamnati da masana harkar lafiya na bayar da tazara a tsakani.

“Abunda ya cece ni shine fara magani da wuri. An yi mun gwaji bayan na fara nuna alamu. Gara mutum ya san matsayinsa tun da wuri.

“Bayan na yi zargin kamuwa, sai na ga akwai bukatar na kare iyalina, don haka sai na kira kwamishinan lafiya wanda ya zo tare da tawagar kwararrun likitoci domin su duba wurin da aka shirya domin na killace kaina,” in ji Okiye.

Kakakin majalisar ya kuma bayyana cewa ya shiga wani hali bayan kamuwa da annobar, amma zantawa da mutane ya bashi kwarin gwiwa.

Kan yadda ya shawo kan cutar da magungunan gargajiya, kakakin ya ce: “na fara shawo kan cutar da magungunan gargajiya da na farin fata.

KU KARANTA KUMA: Fitattun mutanen da ake yi wa hangen mukamin COS bayan mutuwar Kyari

“An daura ni kan magunguna domin magance alamun cutar. Yan kwanaki bayan nan, sai na fara jin dama-dama. Nawa ya fara ne da dan zazzabi. Cutar bata yi mun mugun kamu ba."

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel