Gwamnatin tarayya ta yi gargadi a kan maganin COVID-19 da ake siyarwa a Kano (hoto)

Gwamnatin tarayya ta yi gargadi a kan maganin COVID-19 da ake siyarwa a Kano (hoto)

- Gwamnatin tarayya ta gargadi yan Najeriya a kan guje ma amfani da rigakafin bogi da ake yi a Kano da sunan maganin warkar da annobar Coronavirus

- Ministan labarai, Lai Mohammed ne ya yi wannan gargadi a ranar Talata, 21 ga watan Afrilu

- Ya ce babu wani magani da aka aminta dashi a yanzu da sunan maganin COVID-19

Gwamnatin tarayya a ranar Talata, 21 ga watan Afrilu, ta gargadi yan Najeriya a kan guje ma amfani da rigakafin bogi da ake yi a Kano da sunan maganin warkar da annobar Coronavirus.

Ministan labarai, Alhaji Lai Mohammed, ne ya yi gargadin a babbar birnin tarayya Abuja, lokacin taron kwamitin fadar Shugaban kasa kan COVID-19.

Gwamnatin tarayya ta yi gargadi a kan maganin COVID-9 da ake siyarwa a Kano (hoto)

Gwamnatin tarayya ta yi gargadi a kan maganin COVID-9 da ake siyarwa a Kano (hoto)
Source: Twitter

Ya ce: “A rashin magani ko rigakafin cutar, mataki da ba na magani ba shine babban hanyar dakile yaduwar cutar da kuma kare yan Najeriya.

“Babu mamaki, kun samu labarin tallata wani magani da ake a Kano wanda ake kira da ‘rigakafin COVID-19’.

“Yana nan kalar ruwan dorawa. Babu wanda ya tabbatar da sahihancin maganin. Dan Allah, kada ku sayi maganin daga wajen masu tallata shi.

“A halin da ake ciki, hukumar yada labarai ta kasa NBC, ta dauki matakan hana batar da mutane ta tashoshin labarai ta hanyar gargadinsu da su tsari a matsayinsu na kwararru da kuma yin gaskiya wajen bayar da rahoto kan COVID-19."

KU KARANTA KUMA: Kano: 'Yan sanda sun damke limamai 15 a fadin jihar

A wani labarin mun ji cewa Sakataran kiwon lafiya kasar Birtaniya, Matt Hancock, ya bayyana cewa an samar da rigakafin cutar COVID-19 kuma ranar Alhamis za'a fara gwadawa kan masu cutar.

Masana ilmin Kimiyan jami'ar Oxford ne suka kirkiri rigakafin mai suna ''ChAdOx1 nCoV-19."

Yayinda yake jawabi a taron da aka shirya a fadar shugaban kasar Ingila, 10 Downing Street, Hancock ya ce gwamnatin na iyakan kokarinta wajen samar da rigakafin cutar COVID-19.

Ya ce gwamnatin ta baiwa masana ilmin Kimiyan jami'ar Oxford Yuro milyan 20 (N.9.5bn) domin taimakawa wajen gwajin rigakafin.

Hancock ya ce za'a kara baiwa wasu masana kimiyan na jami'ar Imperial College dake Landan £22.5 million domin nasu binciken.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel