Masu coronavirus a Borno sun zama 4 – Mataimakin Zulum, Kadafur ya tabbatar

Masu coronavirus a Borno sun zama 4 – Mataimakin Zulum, Kadafur ya tabbatar

- Umar Kadafur, mataimakin gwamnan Borno, ya ce a yanzu jahar na da mutane hudu da suka kamu da coronavirus

- Kadafur ya ce sabon wanda ya kamu ya kasance wani matafiyi da aka kama a Gombe bayan sakamako ya nuna yana da ita sai aka tura shi jahar Borno

- A baya Gwamna Babagana Zulum ya sanar da rufe jahar Borno wanda zai fara aiki daga karfe 10:30 na daren ranar Laraba

Ana tsaka da tsoron hauhawar annobar COVID-19, Borno ta ce mutane hudu aka tabbatar suna da coronavirus aa jahar.

Da ya ke magana a taron kwamitin Borno kan COVID-19 a ranar Talata, 21 ga watan Afrilu, Umar Kadafur, mataimakin gwamnan jahar, ya tabbatar da hakan.

Ya kara da cewa an yiwa mutane 48 da suka yi mu’amala da mutum na farko a jahar gwaji.

Masu coronavirus a Borno sun zama 4 – Mataimakin Zulum, Kadafur ya tabbatar
Masu coronavirus a Borno sun zama 4 – Mataimakin Zulum, Kadafur ya tabbatar
Asali: Facebook

Sai dai Kadafur, ya ce sakamakon mutane 44 cikin 48 da ake zargi ya nuna basa dauke da cutar, lamarin da ya kawo sassauci ga tsoron da annobar ya hadda a jahar, jaridar Premium Times ta ruwaito.

Ya kuma bayyana cewa ana jiran sakamakon mutane hudu daga cibiyar kula da hana yaduwar cututtuka ta Najeriya (NCDC).

Legit.ng ta tuna cewa NCDC ta tabbatar da sabbin mutane biyu da suka kamu da COVID-19 a jahar Borno sannan kuma an samu wanda ya mutu a jahar.

KU KARANTA KUMA: Coronavirus: An dakatad da sallar jam'i a masallatai a jahar Nasarawa

Daga bisani sai cibiyar kula da cututtuka ta tabbatar da wani wanda ke cikin matafiya biyar da aka kama a Gombe sannan aka mika shi zuwa Borno inda aka kai shi cibiyar killace wadanda suka kamu a Biu.

A baya mun ji cewa Gwamnan jahar Borno, Umara Babagana Zulum, a ranar Litinin, 20 ga watan Afrilu, ya yi umurnin rufe jahar a wani kokari na hana yaduwar annobar coronavirus a jahar.

Dokar hana fitan zai fara aiki daga karfe 10:30 na daren ranar Laraba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel