Zaman gida zai iya sa 'yan Najeriya su kamu da ciwon 'turombosis'

Zaman gida zai iya sa 'yan Najeriya su kamu da ciwon 'turombosis'

Wani kwararren masanin kimiyyar magunguna, Abiodun Ajibade, ya ce 'yan Najeriya su na cikin hatsarin kamuwa da cutar 'turombosis' sakamakon zaman gida saboda annobar covid-19.

Kwararren, Abiodun Ajibade, ya shawarci 'yan Najeriya su guji jibge jikinsu wuri guda tare da basu shawarar su ke tattaka kafafunsu koda a cikin gidajensu ne domin gudun taruwar jini.

Ajibade, shugaban kungiyar kwararrun masana kimiyyar magani ta Najeriya (PSN) reshen jihar Oyo, ya bayar da wannan shawara ne yayin hirarsa ta wayar tarho da kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN).

Ya ce akwai bukatar gwamnatin tarayya ta nuna damuwarta a kan lafiyar jama'a a yayin da ta saka dokar tilasta su zaman gida saboda annobar covid-19.

A cewar Ajibade, ana samun ciwon 'turombosis' ne sakamakon dunkulewa ko daskarewar jini a cikin jijiya.

Ya bayyana cewa daga cikin abubuwan da ke haddasa ciwon akwai karancin motsi, amfani da wasu magunguna ko bayan an yi wa mutum tiyata.

"Kimanin sati uku kenan da aka saka dokar takaita zirga - zirga domin dakile yaduwa annibar cutar covid-19 Najeriya.

Zaman gida zai iya sa 'yan Najeriya su kamu da cutar 'turombosis'
Ciwon 'turombosis'
Asali: Twitter

"Duk da yin hakan abu ne mai kyau, amma akwai bukatar a duba yanayin lafiyar wasu mutane da rage zirga - zirga zai haifar mu su da turombosis.

"Mutane da yawa za su fara fuskantar alamonin ciwon turombosis, wanda shi ma ciwo ne mai hatsari da barazana ga rayuwa," a cewarsa.

A cewar Ajibade, ciwon turombosis ya kashe mutane da yawa ba tare ma da an san cewa shine silar mutuwarsu ba.

DUBA WANNAN: Dokar hana fita: Mummunan rikici ya barke a Jigawa bayan an harbi yaro mai shekara 10

"An rasa rayuka da yawa sakamakon ciwon turombosis (DVT) ba tare da an san shine sila ba.

"Ana samun toshewar hanyar jini a lokacin ciwon turombosis, lamarin da ke sa a samu karancin jini a wasu muhimman halittun jiki," a cewarsa.

Kwararren ya bukaci kwararru a bangaren lafiya su ke bawa jama'a shawara a kan muhimmancin motsa jiki ga lafiyarsu.

"Dole mu kula da irin illar da zaman gida zai iya haifarwa, dole mu kula da irin illar da dokar kulle za ta iya yi ga lafiyar mu.

"Akwai bukatar mu nesanta da juna, amma akwai bukatar mu ke kula da abincin da za mu ci da kuma motsa jiki," a cewar Ajibade.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng