Coronavirus: An dakatad da sallar jam'i a masallatai a jahar Nasarawa

Coronavirus: An dakatad da sallar jam'i a masallatai a jahar Nasarawa

- Gwamnatin Nasarawa ta haramta sallar jam`i a dukkan masallatai da sauran harkokin ibadah, da na rayuwa da suka shafi hada taron jama`a a jahar

- Har ila yau matakin ya kuma shafi duk wani taron ibadah na mabiya addinin kirista

- Jahar Nasarawa ta dauki matakin ne domin dakile duk wata hanya da zai sa annobar coronavirus bulla a cikinta

Daga cikin kokari da ta ke yin a hana yaduwar annobar coronavirus, gwamnatin Nasarawa ta haramta sallar jam`i a dukkan masallatai da sauran harkokin ibadah, da na rayuwa da suka shafi hada taron jama'a a jahar.

Kakakin gwamnan jahar Nasarawa, Malam Yakubu Lamai wanda ya tabbatar da lamarin, ya ce matakin ya kuma shafi duk wani taron ibadah na mabiya addinin kirista, shashin Hausa na BBC ta ruwaito.

Sai dai har yanzu ba a samu bullar annobar coronavirus ba a jahar Nasarawa wacce ke makwabtaka da Abuja.

Coronavirus: An haramta sallar jam'i a masallatai a jahar Nasarawa

Coronavirus: An haramta sallar jam'i a masallatai a jahar Nasarawa
Source: Twitter

Gwamnatin ta Nasarawa ta ce tana daukar duk matakan da suka dace ne domin dakile bullar cutar a jahar.

KU KARANTA KUMA: Launin fatar jikin wasu likitocin China ya sauya bayan sun warke daga cutar covid-19

Wata sanarwa da gwamnatin ta fitar ranar Talata a Twitter ta ce ta killace wasu mutanen da suka fito daga jihohin Legas da Kano da ke fama da cutar.

A wani labari na daban, mun ji cewa wani bidiyo na wasu mazauna jihar Kano ya jawo cece-kuce a kafafen sada zumuntar zamani.

A bidiyon, an ga matasan jihar na karya dokar nisantar juna da gwamnatin tarayya da ta jihar suka gindaya.

An ga samari cike da filin kwallo suna taka leda inda wasu daban ke zagaye dasu don kallon wasan.

Da karfe 11:10 na daren jiya Litinin ne hukumar kula da cututtuka masu yaduwa ta tabbatar da cewa mutum 23 ne suka sake kamuwa da cutar a jihar Kano.

Hakan ne ya kai jimillar masu cutar zuwa 59 a cibiyar kasuwancin Arewacin Najeriyan.

A ranar 11 ga watan Afirilun 2020 ne jihar Kano ta tabbatar da samuwar cutar a jikin dan jihar.

Bayan kwanaki hudu wanda yayi dai-dai da 15 ga watan Afirilu, an samu mutuwar farko sakamakon cutar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel