Coronavirus: Muna rokon Buhari ya kawo dauki jihar Kano - Ganduje
Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya kirayi gwamnatin tarayya da ta kawo masa dauki na tunkarar annobar cutar coronavirus a jihar.
A rahoton da jaridar Daily Trust ta ruwaito, Ganduje ya mika kokon barar neman tallafin kudi da kuma kayan agaji domin dakile bazuwar cutar corona a jihar da ke Arewacin Najeriya.
Ganduje ya shigar da wannan koke yayin da shugaban cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta Najeriya NCDC, Dr. Chikwe Ihekweazu ya ziyarci fadar gwamnatin Kano a ranar Talata.
Gwamnan wanda ake yiwa lakabi da Khadimul Islama, ya ce a yayin da jihar ke ci gaba da tunkarar annobar corona, basu samu wani tallafi ba daga bangaren gwamnatin tarayya.
Duk da cewa ba a samu bullar cutar ba a yankunan karkara ko kuma wajen birnin Kano, Ganduje ya ce dole a kasance cikin shirin tunkarar lamarin a duk sa'ilin da labari ya sha ban-ban.
Ganduje ya ce muddin aka samu bullar cutar a yankunan karkara na jihar, to kuwa babu shakka akwai kalubale babba da zai rataya a wuyan gwamnatinsa doriya a kan wanda ta ke fuskanta yanzu.
Ya ke cewa, "kawo yanzu ba mu da wata babbar matsala a jihar, amma akwai bukatar mu kasance cikin shiri."

Asali: Facebook
"Muna bukatar karin cibiyar gwaji a jihar, muna bukatar motocin jigilar marasa lafiya da ma'aikatan lafiya gami da na'urorin kariya, muna bukatar tallafin gaske domin tunkarar matsalolin mu cikin gaggawa."
"Kano ce ta uku a jerin jihohi mafi yawan mutanen da cutar corona ta harba baya ga kasancewar ta jiha mafi yawan al'umma a fadin kasar nan. Saboda haka muna bukatar tallafin kudi daga gwamnatin tarayya,” inji shi.
KARANTA KUMA: Mutanen da cutar coronavirus ta kashe sun haura 170,000 a duniya - Alkalumma
A nasa bangaren, Dr Ihekweazu ya ce tawagarsa ta ziyarci jihar Kano ne domin jaddada goyon bayan gwamnatin tarayya a fagen yaki da annobar cutar corona.
Ya yaba da kokarin da gwamnatin Kano ke yi wajen dakile bazuwar cutar a jihar.
Shugaban na NCDC ya ce karuwar cutar covid-19 a jihar Kano ba abin mamaki bane idan akayi la'akari da yawan al'ummar da jihar ta kunsa.
Tun bayan bullar cutar karo na farko a jihar kwanaki goma da suka gabata, an samu mutane 59 da suka harbu yayin da rai ya yiwa mutum daya halinsa.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng