Yanzu-yanzu: Ofishin babban bankin Najeriya CBN ta kama da wuta

Yanzu-yanzu: Ofishin babban bankin Najeriya CBN ta kama da wuta

Labarin dake shigo mana da duminsa na nuna cewa ana gobara a ofishin babban bankin Najeriya CBN, reshen Jos, jihar Plateau a ranar Talata, 21 ga Afrilu, 2020.

Bankin ta tabbatar da hakan a shafinta na Tuwita inda ta bayyana cewa tuni an kashe wutar.

Jawabin yace “An samu karamin gobara a reshen babbar bankin Najerya dake Jos kuma an dakile ta a yau 21 ga Afrilu, 2020.“

KU KARANTA Mutanen da cutar coronavirus ta kashe sun haura 170,000 a duniya - Alkalumma

Wannan shine karo na hudu da manyan ofishohin gwamnatin tarayya a Abuja ke gobara duk da cewa babu maaikata a ofishohin.

An umurci maaikatan gwamnati suyi zamansu a gida saboda dokar ta bacin da gwamnatin tarayya ta sanya a Abuja.

A ranar 17 ga Afrilu, edkwatar hukumar gudanar da zabe ta kasa watau INEC dake birnin tarayya Abuja ta ci bal-bal kuma anyi asarar dukiyoyin gwamnati.

A ranar Larabar, 14 ga watan Afrilu 2020, gobara ta tashi a hedikwatar hukumar yi wa kasuwanci rijista ta kasa (CAC) da ke unguwar Maitama a birnin tarayya, Abuja.

Gobarar ta babbake hawa na karshe a ginin ofishin hukumar CAC mai bene hawa bakwai, tare da lalata muhimman kayayyaki.

Hakazalika a makonni biyu da suka wuce, gobara ta lashe ofishin akawunta janar na tarayya wacce akafi sani da baitul malin gwamnati dake Abuja.

Bayan gobarar ta kwashe lokaci tana ci bal-bal karamin ministan kasafi da tsare-tsare na kasa, Prince Clem Agba, ya yi magana a kan gobarar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel