Mun yi wa mutane 8,003 gwajin cutar COVID-19, inji hukumar NCDC
Mutane fiye da 600 ne su ka kamu da cutar COVID-19 a Najeriya kamar yadda alkaluma su ka tabbatar. Hukumar NCDC ta yi karin haske game da wannan mummunar annoba.
Hukumar da ke da alhakin takaita yaduwar cuta a kasar nan ta NCDC ta bayyana cewa ta yi wa mutane 8, 003 gwaji a halin yanzu.
Daga cikin mutane 9, 233 da su ka bukaci ayi masu gwaji, an iya samun 8, 003 daga cikinsu. Hakan ya nuna an tuntubi kusan 90% na wadanda ake zargin su na dauke da cutar.
Rahoton da hukumar NCDC ta fitar a ranar Litinin, 20 ga watan Afrilu, 2020, ya nuna cewa wannan cuta ta shiga jihohi 22 da kuma babban birnin tarayya Abuja a shekarar nan.
NCDC ta ce 3% rak na wadanda su ka kamu da wannan cuta ne su ke mutuwa a daidai wannan lokaci. Mutane 22 kuma su ka mutu yayin da aka sallami 188 daga gadajen asibiti.
KU KARANTA: Babu shiga babu fita bayan COVID-19 ta kashe mutum 1 a Borno
Borno, Sokoto da Abia su na cikin jihohin da wannan cuta ta shiga daga baya-bayan nan. Wannan ya nuna cewa a wasu jihohi 14 ne kawai ba a samu bullar wannan cuta a kasar ba.
Wannan rahoto ya kuma nuna cewa maza sun fi kamuwa da COVID-19 a Najeriya.
Alkaluma sun tabbatar da cewa 70% na wadanda cutar ta kama maza ne (mutane kimanin 465).
Haka zalika an fahimci cewa wannan cuta ta fi kama wadanda su ke tsakanin shekara 31 zuwa 40. Masana kiwon lafiya sun dai tabbatar da cewa cutar ta fi yin illa a kan tsofaffi.
A makon jiya ne COVID-19 ta kashe hadimin shugaban Najeriya Abba Kyari ya rasu. Shugaban kungiyar kiristoci na PFN ya aikawa Buhari wasika kan mutuwar hadimin na sa.
A jiya mutane 23 aka samu wadanda su ke dauke da Coronavirus a jihar Kano. A gwajin da NCDC ta yi jiya, ba a samu ko da mutum guda da ke dauke da wannan cuta a Legas ba.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng