Coronavirus: Gwamna Zulum ya rufe jahar Borno na tsawon kwanaki 14

Coronavirus: Gwamna Zulum ya rufe jahar Borno na tsawon kwanaki 14

- Gwamna Babagana Zulum, ya yi umurnin rufe jahar Borno na tsawon kwanaki 14

- Hakan na daga cikin kokarin da gwamnatin ke yi na hana yaduwar annobar COVID-19 a jahar

- Ya ce a wannan lokaci ana bukatar mutanen jahar su kasance a gida, sannan a rufe duk wani harkoki na kasuwanci da sauransu

Gwamnan jahar Borno, Umara Babagana Zulum, a ranar Litinin, 20 ga watan Afrilu, ya yi umurnin rufe jahar a wani kokari na hana yaduwar annobar coronavirus a jahar.

A wani jawabi na fadin jahar, Zulum ya ce: “Da karfin ikon da aka bani, na sa hannu a wani oda, wanda ke kaddamar da Covid-19 a matsayin cuta mai hatsari.“

"Don haka, na yi umurnin rufe jahar wanda zai haramta duk wani zirga-zirga a jahar Borno na tsawon kwanaki 14, fara daga karfe 10:30 na safiyar ranar Laraba, 22 ga watan Afrilu, 2020.“

"Dukkanin al’umman jahar Borno su kasance a gidajensu. Hakan na nufin hana duk wani zirga-zirga, yayinda za a rufe dukkanin ofishoshi da kasuwanci a jahar Borno a wannan lokacin. “

“An sanar da hukumomin tsaro kan dokar."

Coronavirus: Gwamna Zulum ya rufe jahar Borno na tsawon kwanaki 14
Coronavirus: Gwamna Zulum ya rufe jahar Borno na tsawon kwanaki 14
Asali: Twitter

Gwamnati za tayi amfani da wannan lokaci na hana zirga-zirga wajen ganowa da killace mutanen da suka yi mu’amala da mutum na farko da aka samu da cutar.

KU KARANTA KUMA: Gwamnan Borno ya jagoranci Tawaga sun ziyarci Dangin Abba Kyari a Bama

Sai dai kuma, kwamitin jahar kan kula da hana yaduwar COVID-19 ya gano mutane 97 da suka yi hulda da mai cutar wanda ya mutu.

Shugaban kwamitin, Alhaji Umar Kadafur, wanda ya kuma kasance mataimakin gwamnan jahar, ne ya bayyana hakan a taron manema labarai a Maiduguri.

A wani labari na daban, mun ji cewa marasa lafiyar da ke ziyartar wasu asibitoci ma su zaman kansu a jihar Legas sun samu sakonnin bukatar su killace kansu saboda su na cikin hatsarin kamuwa da kwayar cutar covid-19.

Asibitocin da yanzu gwamnatin jihar ta rufesu sune kamar haka; St Nicholas, reshen Lagos Island branch; First Cardiology Consultants Hospital da ke Ikoyi, inda Abba Kyari ya mutu, da St Edwards Hospital da ke Ajah.

Sauran sune; Vedic Lifecare Hospital da ke Lekki; County Hospital, Ogba da Premier Specialist Hospital da ke Victoria Island.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng