Boss: Babu maganar kawo karshen cutar COVID-19 nan kusa tukuna

Boss: Babu maganar kawo karshen cutar COVID-19 nan kusa tukuna

A yayin da ake cigaba da yaki da annobar Coronavirus, fadar shugaban kasar Najeriya ta fito ta yi magana game da halin da ake ciki a kasar inda cutar ta ke cigaba da yaduwa.

Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya yi jawabi mai razanarwa a ranar Litinin, 19 ga Afrilun 2020 inda ya ce har yanzu ba a kusa kai ga kawo karshen wannan annoba ba.

Jaridar The Cable ta ce sakataren gwamnatin ya yi wannan bayani ne wajen wata zantawa da kwamitin shugaban kasa na yaki da annobar COVID-19 ta yi da ‘yan jarida jiya a Abuja.

Sakataren na gwamnatin Najeriya ya yi kira ga jama’a su bi dokokin da hukumomi su ka kafa domin takaita yaduwar COVID-19, inda ya ce gwamnati na bakin kokarin yaki da annobar.

Shugaban kwamitin ya ce:“Ganin yadda masu dauke da cutar nan su ka karu a makon jiya, kwamitin PTF ta na lura da cewa ba mu ka kai ga ganin karshen wannan annoba a Najeriya ba.

Don haka dole mu zage dantse wajen yin gwaji da killace masu dauke da cutar, tare da bin wadanda ake zargin sun kamu, da kuma kula da wadanda cutar ta kama har su warke.”

KU KARANTA: Dalilin da ya sa aka samu damar yi wa Abba Kyari sallar jana’iza

Boss: Babu maganar kawo karshen cutar COVID-19 nan kusa tukuna
Mutane fiye da 600 sun kamu cutar COVID-19 a Najeriya
Asali: Twitter

Karuwar yaduwar cutar a tsakanin jihohi ya kara nuna muhimmancin ‘yan kasa su natsu saboda kalubalen da ke gabanmu.” Mustapha ya ce yanzu lokaci ne da ake bukatar hadin-kai.

“Dole mu yi bakin kokari ko ta wani hali mu sauko da tashin da alkalumar masu dauke da wannan cuta ta ke yi, mu kuma dawo da kasarmu a cigaba da gudanar da harkoki.” Inji sa.

Haka kuma Mustapha a matsayinsa na shugaban PTF ya yi magana game da saba dokar da aka yi wajen bizne Abba Kyari. A cewarsa sun yi da-na-sanin wannan kuskure da aka yi.

“Mun koyi darasinmu, kuma an dauki matakan da su ka dace. Mu na tabbatarwa duk ‘yan Najeriya cewa za mu kare lafiyarsu, kuma PTF ta shirya ganin karshen annobar nan.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel