Annobar Corona: Gwamna ya fara biyan matasan jaharsa N30,000 a Najeriya

Annobar Corona: Gwamna ya fara biyan matasan jaharsa N30,000 a Najeriya

Gwamnatin jahar Cross Rivers a karkashin jagoran gwamnan jahar, Farfesa Ben Ayade ta kaddamar da rabon kudaden tallafi na naira dubu talatin-talatin ga matasan jahar.

Talabijin na Channels ta ruwaito gwamnatin za ta biya matasan dake cin gajiyar tsarin tallafi na YESSO, alawus na N30,000 a kowanne wata don rage musu radadin fitinar COVID-19.

KU KARANTA: Batun sauya ma jami’ar jahar Imo suna zuwa jami’ar Abba Kyari karya ne – Gwamna

Kwamishinan cigaban jahar, Inyang Asibong ne ya bayyana haka yayin kaddamar da biyan kudin, inda yace aikin zai gudana ne tare da hadin gwiwar babban bankin duniya.

Da yake kaddamar da rabon a karamar hukumar Akampa, kwamishinan yace manufar shirin shi ne tallafa ma marasa karfi a jahar domin su samu biyan bukatunsu duk halin da ake ciki.

Ya kara da cewa gwamnatin za ta biya kudin ga matasan dake sadaukar da kansu wajen ayyukan sa kai kamar aikin tsaftace gari, kwashe kwatoci, kula da zaizayar kasa da sauransu.

Haka zalika a kokarinsa na yaki da yaduwar cutar Coronavirus a jahar Cross Rivers, Gwamna Ayade ya umarci duk mazauna jahar su dinga sanya abin rufe hanci da baki.

Annobar Corona: Gwamna ya fara biyan matasan jaharsa N30,000 a Najeriya

Annobar Corona: Gwamna ya fara biyan matasan jaharsa N30,000 a Najeriya
Source: Facebook

Gwamnan ya ce gwamnatinsa ba za ta amince ma wani ya fito daga gida ba tare da yana sanye da abin rufe fuskar ba, idan kuma ba haka ba mutum zai fuskanci hukunci.

Zuwa yanzu dai babu rahoton bullar cutar a jahar, amma jahar na makwabtaka da kasar Kamaru, wanda ke da mutane 1000 da suke dauke da cutar, yayin da wasu kuma suka mutu.

A hannu guda kuma gwamnatin jahar Sakkwato ta sanar da bullar mugunyar cutar Coronavirus a jahar.

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ne ya bayyana haka da kansa cikin wani jawabi da ya yi ma al’ummar jahar Sakkwato inda ya fara da fadin “Innalillahi wa Inna Ilaihi raji’un”

Ya cigaba da jawabinsakamar haka: “Jama’an jahar Sakkwato, tare da alhini da damuwa nake sanar da ku cewa annobar COVID-19, ma’ana Coronavirus ta shigo jahar Sakkwato. A yanzu haka mun fara shirin killace mutumin a wurin killacewa dake Amanawa.”

Gwamnan ya ce a yanzu haka mutumin dake dauke da cutar ya fara samun kulawa a asibitin koyarwa ta jami’ar Usmanu Danfodiio dake jahar Sakkwato.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel