El-Rufai ya na aiki daga inda ya killace kansa, bai shiga gargara ba – inji Dattijo
Jita-jita sun fara yawo a gari cewa jikin gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya tabarbare bayan ya kamu da muguwar cutar Coronavirus a cikin watan Maris.
Gwamnatin Kaduna ta fito ta yi magana game da halin da mai girma Nasir El-Rufai ya ke ciki. Gaskiyar lamarin shi ne El-Rufai ya na samun lafiya ba kamar yadda ake rayawa ba.
Shugaban ma’aikatan fadar gwamnan na jihar Kaduna, Muhammad Sani Dattijo ya karyata rade-radin da ake yi na cewa mai gidansa ya shiga gargara, har an kai shi bangaren ICU.
Legit.ng ta tabbatar da cewa Malam Sani Dattijo ya bayyana haka ne a magana da ya yi a shafinsa na sada zumunta na zamani na Tuwita a ranar Litinin, 20 ga watan Afrilun 2020.
Sani Dattijo ya nuna hotonsa da gwamnan yayin da su ke zantawa a wani taro da aka yi ta kafar sadarwa ta zamani. Hadimin ya nuna El-Rufai ya na nan da ransa kuma cikin lafiya.
KU KARANTA: An sallami wadanda su ka warke daga Coronavirus a jihar Kaduna
Babban hadimin gwamnan ya fito ya rubuta: “Malam Nasir El-Rufai da karfe 2:06 na rana a ranar (jiya) 20 ga watan Afrilu. A raye kuma ya na lafiya. Ya na aiki daga inda ya kebe kansa.”
Tsohon kwamishinan wanda yanzu ya zama shugaban ma’aikatan gidan gwamnati ya kara da cewa: “Masu maganar an kai shi sashen ICU, sai kun riga shi lekawa in Allah ya so.”
Jigon na gwamnatin El-Rufai ya yi duk wannan jawabi ne a shafin na sa na Tuwita @Dattijo. Sani Dattijo ya fito ya bayyana tattaunawarsu da gwamnan ne bayan ‘yan mintuna kadan.
A ranar 28 ga watan Maris, Nasir El-Rufai ya shaidawa mutane cewa ya yi gwaji kuma an gano cewa ya na dauke da cutar COVID-19. Makonni uku bayan nan har yanzu bai warke ba.
Sauran gwamnonin da su ka kamu da wannan cuta sun samu sauki a yanzu. Takwarorin El-Rufai da cutar nan ta kama su ne Seyi Makinde da Bala Mohammed na jihohin Oyo da Bauchi.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng