COVID-19: Babu dokar da ta haramta mana bada gawa inji Gwamnatin Legas

COVID-19: Babu dokar da ta haramta mana bada gawa inji Gwamnatin Legas

A ranar Juma’ar da ta wuce ne shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasar Najeriya, Abba Kyari ya mutu a wani asibiti a Legas a sanadiyyar kamuwa da cutar nan ta Coronavirus.

Kwamishinan lafiya na jihar Legas, Akin Abayomi, ya yi magana game da dalilin da ya sa aka bada gawar Malam Abba Kyari ga iyalinsa domin ayi mata wanka da Sallar Jana’iza.

Idan ba ku manta ba kwanakin baya, ministan yada labaran Najeriya, Alhaji Lai Mohammed, ya ce ba za a rika bada gawar wadanda su ka mutu sakamakon fama da cutar COVID-19 ba.

Sai dai kwamishinan na Legas ya ce za a bada gawar wadanda cutar ta kashe bayan an tsarkake jikinsu daga kwayar cutar. Wannan ya zama akasin matsayar gwamnatin tarayya.

Kwamishinan ya ce: “Hanyar da ake bi game da mutuwa daga COVID-19 shi ne za a tsarkake jikin mamacin daga cutar. Daga nan sai a sa gawarsa a cikin wata jaka ta musamman.”

KU KARANTA: An rufe asibitin da Abba Kyari ya mutu ya na jinya a Legas

COVID-19: Babu dokar da ta haramta mana bada gawa inji Gwamnatin Legas
Malam Abba Kyari ya mutu ya na da shekaru 67 a Legas
Asali: Depositphotos

Mu na sa gawar ne a cikin jakunkuna biyu, sai a rufe ta a cikin makara, ita kanta makarar ana rufe ta tsaf.” Abayomi ya ce haka ake yi wa wadanda wannan annoba ta kashe su.

Haka zalika kwamishinan na gwamnatin Babajide Sanwo-Olu ya kara da cewa sharadin da hukuma ta sa shi ne ba za a amince da mutum 25 wajen jana’iza da bizne gawar ba.

“A halin yanzu babu wata doka da ta hana mu mika gawar mamaci ga ‘yanuwansa; sai dai za a yi wannan ne ta yadda ‘yanuwan mamacin ba za su kamu da cutar ba.” Inji kwamishinan.

Kwamishinan lafiyan ya ce su na tabbatar da cewa jama’a ba su saba dokar da aka kafa ta hana cinkoson jama’a a wuri guda ba. Wannan zai takaita yaduwar wannan cuta ta COVID-19.

Tuni dai aka bizne marigayin a wata makabarta da ke garin Abuja bayan shehin malami kuma ministan gwamnatin tarayya Isa Ali Ibrahim Pantami ya yi masa sallar jana’iza a ranar Asabar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng