Babbar magana: Gwamnati za ta gurfanar da wasu ma su cutar covid-19

Babbar magana: Gwamnati za ta gurfanar da wasu ma su cutar covid-19

Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-olu, ya ce gwamnatinsa za ta gurfanar da wasu ma su dauke da kwayar cutar covid-19 da su ka yi karya a kan bayanan tafiye - tafiyensu.

Sanwo-olu ya bayyana hakan ne a gidan gwamnatin jihar Legas da ke Marina yayin ganawarsa da manema labarai ranar Litinin, kamar yadda jaridar 'The Nation' ta rawaito.

"Irin wadannan marasa lafiya sun cutar da ma'aikatanmu na lafiya, a saboda haka za mu gurfanar da su.

"Tuni mun samu sunayen wasu daga cikinsu, kuma za mu gurfanar da su, saboda ba iya kansu su ka cutar ba, sun cutar da mutane da dama.

"A saboda haka, ina kira ga ma'aikatanmu na lafiya a kan su tona asirin irin wadannan marasa lafiya da ke boye gaskiyar bayanan tafiye - tafiyensu," a cewar gwamnan.

Babbar magana: Gwamnati za ta gurfanar da wasu ma su cutar covid-19
Gwamnan jihar Legas; Babajide Sanwo-olu
Asali: Twitter

A wani labarin da ya shafi Kano da Legit.ng ta wallafa, gwamnatin jihar ta yi watsi da rade-radin da ke yawo kan cewa mutane na mutuwa birjik a jahar a 'yan kwanakin nan.

DUBA WANNAN: An samu muhimman bayanai a kan mutumin da cutar covid-19 ta kashe a jihar Borno

A wani rabutu da ma’aikatar lafiya ta jahar ta wallafa a shafinta na Twitter, ta bayyana cewa babu gaskiya a cikin jita-jitan.

Ta bayyana hakan a matsayin aikin masu yada zantuka marasa tushe.

Ma’aikatar lafiyar ta jaddada cewa ta na daukar matakai da suka kamata domin ganin ta dakile annobar COVID-19 a jahar. Ta kuma ce ta na da karfin gwiwa a kan yaki da take yi da annobar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel