Gwamna Uzodinma zai sauya sunan jami'ar jiharsa da na marigayi Abba Kyari

Gwamna Uzodinma zai sauya sunan jami'ar jiharsa da na marigayi Abba Kyari

- Gwamna Hope Uzodinma na jahar Imo, ya bayyana cewa yana shirin sauya sunan jami’ar jahar Imo, zuwa sunan Abba Kyari

- Ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, 20 ga watan Afrilu, lokacin da mahukuntan jami’ar suka kai masa ziyara a gidan gwamnati a Owerri

- Uzodinma ya ce Kyari ya taka gagarumin rawar gani wajen yantad da jahar Imo

Gwamnan jahar Imo, Hope Uzodinma ya bayyana cewa yana shirin sauya sunan jami’ar jahar Imo, zuwa sunan Abba Kyari, marigayi shugaban ma’aikatan shugaban kasa.

An tattaro cewa gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, 20 ga watan Afrilu, lokacin da mahukuntan jami’ar suka kai masa ziyara a gidan gwamnati a Owerri, jaridar Premium Times ta ruwaito.

Gwamna Uzodinma zai sauya sunan jami'ar jiharsa da na marigayi Abba Kyari
Gwamna Uzodinma zai sauya sunan jami'ar jiharsa da na marigayi Abba Kyari
Asali: UGC

A cewar wata sanarwa daga kakakinsa, Oguwuike Nwachuku, gwamnan ya bayyana cewa Kyari ya taka gagarumin rawar gani wajen yantad da jahar Imo.

Ya ce babu wani karamci da ya yi girma ga mutumin da ya mutu wajen yiwa kasa hidima.

KU KARANTA KUMA: Azumin bana: An shirya wurin da Sheikh Ahmed Gumi zai gudanar da Tafsiri

Sai dai gwamnan bai yi karin haske a kan abunda ya ke nufi da yancin Imo ba.

A wani labarin kuma, mun ji cewa Kwamishinan aiyuka na jihar Kano, Mu'azu Magaji, da gwamna Ganduje ya tube ya yi magana a karon farko tun bayan sanar da sauke shi daga mukaminsa a ranar Asabar.

Gwamna Ganduje ya tube kwamishinan ne bisa wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na dandalin sada zumunta, wato 'facebook', a kan mutuwar Abba Kyari.

Jama'a da dama sun fassara rubutun Magaji a matsayin nuna murna da mutuwar Kyari, lamarin da ya sa har gwamna Ganduje ya sallame shi jim kadan bayan wallafa rubutun.

Sai dai, a jawabin da tsohon kwamishinan ya fitar ranar Lahadi, ya ce an yi wa rubutunsa mummunar fassara tare da bayyana cewar shi ba murnar mutuwar Kyari ya ke yi ba.

A cikin jawabin, Magaji ya bayyana cewa babu yadda za a yi a matsayinsa na Musulmi ya yi murnar mutuwar wani mutum.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel