An samu muhimman bayanai a kan mutumin da cutar covid-19 ta kashe a jihar Borno

An samu muhimman bayanai a kan mutumin da cutar covid-19 ta kashe a jihar Borno

Majalisar dinkin duniya (UN) ta ce ma'aikacinta da cutar covid-19 ta hallaka a jihar Borno bashi da tarihin yin bulaguro zuwa wajen jihar Borno.

Edward Kallon, jagoran harkokin aiyukan taimako na UN a Najeriya, ya ce su na kokarin bin sahun duk mutanen da marigayin ya yi mu'amala da su kafin mutuwarsa.

A ranar Lahadi ne rahotanni su ka bayyana cewa wani ma'aikacin UN ya mutu a asibitin koyarwa na jami'ar Maiduguri bayan an kwantar da shi sakamakon nuna alamomin rashin lafiya irin na cutar covid-19.

"Marigayin ya sadaukar da rayuwarsa ne wajen taimakon mutanen da ke zaune a sansanin 'yan gudun hijia.

"Bashi da tarihin yin bulaguro zuwa wajen jihar Borno.

"Hukumomin aiyukan jin kai a karkashin hukumar lafiya ta duniya (WHO) su na aiki tare da NCDC, gwamnatin jihar Borno, ma'aikatar lafiya ta kasa da sauran ma su ruwa da tsaki wajen bin sahun mutanen da ya yi mu'amala da su," a cewar Kallon.

An samu muhimman bayanai a kan mutumin da cutar covid-19 ta kashe a jihar Borno

Buhari da Zulum
Source: Twitter

Mutuwar mutumin ta saka jihar Borno cikin jerin jihohin Najeriya da aka tabbatar da bullar annobar cutar covid-19.

A wani labarin mai nasaba da wannan da Legit.ng ta wallafa, gwamnan jihar Jigawa, Mohammed Badaru Abubakar, ya yi karin bayani a kan tabbatar da samun bullar annobar cutar covid-19 a jiharsa a karon farko.

DUBA WANNAN: 'Yan arewa 9 da ake kyautata zaton daga cikinsu Buhari zai zabi madadin Abba Kyari

A daren ranar Lahadi ne cibiyar kula da cututtuka ma su yaduwa ta kasa (NCDC) ta fitar da sanarwar cewa annobar ta bulla jihar Jigawa yayin sanar da karin mutane 86 da su ka kamu da kwayar cutar a Najeriya.

A wata ganawa da ya yi da manema labarai ranar Lahadi, gwamna Badaru ya yi karin haske a kan mutumin da aka tabbatar ya na dauke da kwayar cutar a jiharsa.

Badaru ya bayyana cewa mutumin da aka tabbatar ya na dauke da kwayar cutar, dan kasuwa ne da ke fita fatauci zuwa kudancin Najeriya daga karamar hukumar Kazaure.

Mutumin, wanda keda shagon sayar da sutura, ya fara nuna alamomin kwayar cutar covid-19 bayan dawowarsa daga kudancin Najeriya, kamar yadda ya saba fita harkokinsa na kasuwanci, a cewar Badaru.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel