Hukumar KEDC ta dakatar da yanke wutar lantarki a jahar Kaduna saboda Corona

Hukumar KEDC ta dakatar da yanke wutar lantarki a jahar Kaduna saboda Corona

Hukumar wutar lantarki ta Kaduna, Kaduna Electric ta dakatar da yanke wutar lantarki a jahar Kaduna da jahohin da take raba ma wuta har sai an shawo kan annobar COVID-19.

Daily Trust ta ruwaito shugaban sashin watsa labaru na KEDC Abdulazeez Abdullahi ne ya bayyana haka a ranar Litinin yayin mika taimakon kayan tallafin ga gwamnatin Kaduna.

KU KARANTA: Kisan mutane 47 a Katsina: Buhari ya yi alkawarin ramuwar gayya a kan yan bindiga

Malam Abdulaziz ya ce kamfaninsu ta ware naira miliyan 30 domin taimaka ma jama’an jahohin Kaduna, Zamfara, Sakkwato da Kebbi da abinci, musamman talakawa da gajiyayyu.

Abdulaziz ya ce sun shirya hakan ne don taimaka ma kokarin da gwamnatin jahar take yi na rage ma jama’a radadin halin da suke ciki sakamakon cutar Coronavirus.

Hukumar KEDC ta dakatar da yanke wutar lantarki a jahar Kaduna saboda Corona

Hukumar KEDC ta dakatar da yanke wutar lantarki a jahar Kaduna saboda Corona
Source: Twitter

“Mun yarda a matsayinmu na kamfani mai zaman kansa muna da rawar da za mu taka a wannan lamari shi yasa muka bayar da tallafin buhuna 500 na shinkafa, buhuna 400 na semovita, kwali 100 na indomie da katan 100 na man gyada.

“Muna fata za’a yi amfani da wadannan kayan abinci wajen raba ma wadanda suka cancanta, kuma muna fatan samun nasara a kan wannan annoba nan bada jimawa ba.” Inji shi.

Daga karshe Abdulaziz ya tabbatar ma jama'a samun tsayayyen wutar lantarki a wannan lokaci, sa’annan ya nemi jama’a su cigaba da bin dokokin kiwon lafiya don kare kansu.

Da yake karbar kayan a madadin gwamnatin jahar Kaduna, sakataren ofishin sakataren gwamnatin jahar, Mohammed Bashir ya ce gwamnatin ta kashe N500m wajen bayar da tallafi.

Sai dai yace gwamnati ba za ta iya daukan nauyin tallafawa a wannan lokaci ita kadai ba, don haka ya kara kira ga kamfanoni masu zaman kansu da masu kudi su taimaka ma jama’a.

A hannu guda gwamnatin Kaduna ta sanar da yiwuwar sake duba dokar ta bacin da ta sanya da nufin kara saussauta shi domin jama;a su samu walwala.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Nigeria

Online view pixel