An sake sallamar karin masu COVID-19 su 4 a Lagas

An sake sallamar karin masu COVID-19 su 4 a Lagas

Gwamnatin jahar Lagas ta sallami karin mutane hudu da ke dauke da COVID-19 daga cibiyarta na killace wadanda suka kamu, a yanzu jumular marasa lafiya 98 kenan suka warke a jahar.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ma’aikatar lafiya ta jahar ta wallafa a shafinta na Twitter, a ranar Lahadi, 19 ga watan Afrilu.

An sallami uku daga cikin marasa lafiyan ne daga cibiyar killace masu cutar na Yaba, yayinda sauran mutum daya kuma daga asibitin koyarwa na Lagas, bayan sun warke.

Sannan sau biyu a jere gwaji na nuna basa da cutar.

Ta bayyana cewa an saki marasa lafiyan wadanda dukkansu maza ne, domin su sadu da yan uwansu.

Gwamnatin jahar ta roki mazauna jahar da su zauna a gida domin tsira daga cutar da kuma samun nasarar kakkabe cutar a Lagas.

A gefe daya, hukumar dakile cutuka masu yaduwa a Najeriya NCDC ta tabbatar cewa zuwa yanzu mutum 627 suka harbu da cutar corona a kasar.

Hakan na zuwa ne bayan da a ranar Lahadi da daddare NCDC ta sake sanar samun karin mutum 86 da suka kamu da cutar, a ranar Litinin, 20 ga watan Afrilu a kasar.

A shafinta na Tiwita, hukumar ta NCDC ta bayyana cewa a yanzu cutar corona ta yadu a jihohin kasar 21 har da babban birnin Abuja.

KU KARANTA KUMA: Coronavirus ta kawo tsaiko a shari’u 155,757 a Najeriya

Daga cikin na bayan nan da ta sanar, 70 daga cikinsu sun fito ne daga Legas sai bakwai a Abuja da uku a Katsina da wasu karin uku a Akwa Ibom sai mutum 1 a Jigawa da 1 Bauchi da kuma karin wani a Borno.

Karon farko ke nan da aka samu bullar wannan annoba a jihohin Jigawa da Borno.

Ana jin wadannan ne alkaluma mafi yawa na mutanen da suka kamu da cutar corona rana daya a Najeriya da hukumar ta fitar, tun bayan fara samun annobar ranar Alhamis, 27 ga watan Fabrairu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng