Kwamitin COVID-19 a Katsina ya kashe miliyan N24.6 wajen yiwa masallatai da cocina feshi

Kwamitin COVID-19 a Katsina ya kashe miliyan N24.6 wajen yiwa masallatai da cocina feshi

Kwamitin agajin gaggawa kan COVID-19 a jahar Katsina, ya ce ta fadada naira miliyan 24.6 wajen yiwa masallatai da cocina feshi da kuma samar da kayayyakin tsaftacce wuri.

Shugaban kwamitin kuma mataimakin gwamna, Mannir Yakubu, ya bayyana cewa an kashe naira miliyan 19.1 wajen yin feshi.

Sannan aka kashe naira miliyan 5.4 wajen siyan kayayyakin tsafta da aka rarrabawa masallatai da cocina.

Yayinda ya ke rabe-raben abunda aka kashe dalla-dalla na sama da naira miliyan 207 da gwamnati ta samu a matsayin tallafi, ya ce horar da likitoci 66 da malaman jinya 102, ya ja naira miliyan 3.7.

Kwamitin COVID-19 a Katsina ya kashe miliyan N24.6 wajen yiwa masallatai da cocina feshi
Kwamitin COVID-19 a Katsina ya kashe miliyan N24.6 wajen yiwa masallatai da cocina feshi
Asali: Facebook

“Ayyukan kwamitin da aka kafa domin wayar da kan jama’a ya ja naira miliyan 4.5, yayinda kudin alawus din likitoci da aka kwaso cibiyar killace wadanda suka kamu a duk wata ya ja naira miliyan 10.2,” in ji shi.

Ya ce an kuma amince da karin naira miliyan 3.5 domin wayar da kan mambobin kungiyar yan kasuwa na jahar.

KU KARANTA KUMA: ‘Yan Majalisar dokokin Oyo sun amince da ragin albashi domin yaki da COVID-19

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa rabe-raben yadda kwamitin ta kashe kudaden na zuwa ne bayan masu ruwa da tsaki sun yi caccaka a kan kudaden da aka samu da kuma abunda aka yi amfani da su.

A wani labarin kuma, mun ji cewa, tuni dai gwamnati ta fara kwashe Almajirai daga birnin Kano zuwa mahaifarsu.

Gwamnatin Kano ta dauki wannan mataki a ci gaba da yunkurin da take yi na dakile yaduwar cutar coronavirus, wadda ta bulla a jihar makonni kadan da suka gabata.

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito, furucin wannan mataki ya fito ne daga bakin Gwamnan jihar, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

Ganduje ya bayar da shaidar hakan a ranar Lahadi yayin ganawa da kwamitin da ke tattara tallafi da kuma gudunmuwar da aka samu ta rage radadin annobar coronavirus.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel