Yadda Marigayi Abba Kyari ya dage wajen yaki da Coronavirus kafin ya mutu

Yadda Marigayi Abba Kyari ya dage wajen yaki da Coronavirus kafin ya mutu

Sai bayan cikawar Malam Abba Kyari ne labarai su ka rika bayyana inda aka ji irin ayyukan alherin da aka ce ya yi. Kyari ya na cikin wadanda COVID-19 ta kashe a Najeriya.

Mai girma gwamnan jihar Bauchi, Bala Abdukadir Mohammed, ya ce Marigayi Abba Kyari ya taimaka masa da wasu shawarwari a lokacin da su ke fama da cutar Coronavirus.

Gwamna Bala Mohammed wanda ya warke daga wannan cuta daga baya, ya bayyana Abba Kyari a matsayin ‘dan Najeriyan kwarai, sannan ‘danuwa kuma Surukin mutanen Bauchi.

Bala Mohammed ya bayyana wannan ne a wata wasikar ta’aziyya ta musamman da ya aikawa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari jiya game da rashin babban hadimin na sa.

“Mu a jihar Bauchi mu na tare da kai wajen jimamin wannan babban rashi da makokin mutuwar shugaban ma’aikatan fadarka. (Kyari) uba ne, kuma ‘danuwa da suruki a wurinmu."

KU KARANTA: Ibrahim Babangida ya yabi Marigayi Abba Kyari a sakon ta’aziyya

“Na yi waya ta salula da Malam Abba (Kyari), inda ya bani shawarwarin da su ka yi mani matukar amfani wajen samun lafiya lokacin da aka killace mu, mu na jinya.” Inji gwamna Bala.

Ya ce: “Don haka ina tarayya da kai wajen wannan bakin ciki da ka ke fama da shi. Za mu cigaba da koyi da tarbiyyarsa, da kishi da yi wa kasa bauta. Allah ya ba shi Aljanna ta Firdaus.”

Simon Kolawole wanda ya na cikin wadanda su ka san Marigayin ya bayyana irin kokarin da ya rika yi a bayan fage na ganin cewa Najeriya ta shawo kan wannan muguwar cuta.

Kolawole ya ke cewa Kyari ya dage da bibiyar yawan na’urori da gadajen da ake da su a asibitocin kasar tare da duba tasirin annobar ga tattalin Najeriya kafin wannan cutar ta kama shi.

A cikin karshen watan Maris ne aka yi wa Kyari gwaji aka kuma gano ya kamu da COVID-19. Bayan ya fara samun lafiya kuma kwatsam sai jikinsa ya tabarbare, a karshe ya cika.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel