Kyari bai bari surutan Jama’a ya karkatar da shi daga tafiyar Buhari ba - NGF

Kyari bai bari surutan Jama’a ya karkatar da shi daga tafiyar Buhari ba - NGF

Bayan rasuwar Abba Kyari a ranar Juma’ar nan, mutane sun fito su na ta mika ta’aziyyarsu. Har shugabannin kasashen waje sun kira Muhammadu Buhari sun yi masa ta’aziyya.

Kungiyar gwamnonin Najeriya a karkashin shugabanta Dr. Kayode Fayemi, ta yi magana game da rashin hadimin shugaban kasar Najeriyar da aka yi wanda ya girgiza fadin kasar.

Dr. Kayode Fayemi ya rubuta wasika a madadin sauran gwamnonin Najeriya inda ya bayyana cewa Abba Kyari bai bari abin da jama’a ke fada a waje ya canza masa akida ba.

Shugaban gwamnonin na Najeriya ya ke cewa ka-ce-na-cen jama’a bai sa Marigayi Abba Kyari ya bar tafarkin da aka san shi a kai na tsayawa a kan akidun shugaba Buhari ba.

A wannan wasika da mu ka samu labarinta a ranar 19 ga Afriku, kungiyar NGF ta ce har Malam Kyari ya bar Duniya, ya na cikin kusoshin gwamnatin Muhammadu Buhari.

KU KARANTA:

Kyari bai bari surutan Jama’a ya karkatar da shi daga tafiyar Buhari ba - NGF
Shugabannin kasashe daga ketare sun yi wa Muhammadu Buhari ta’aziyya
Asali: UGC

KU KARANTA: Abba Kyari: Mun yi rashi, mun yi rashi inji Ismail Isa Funtua

“Cikin hikima da hangen nesa, Kyari ya kafa dangantaka mai kyau tsakanin shugaban kasa da ministoci, kuma ya karfafa dankon da ke tsakanin kungiyarmu da gwamnatinka.”

NGF ta aika wannan wasika ne ga shugaban kasa ta na mai cewa: “Marigayi Abba Kyari ya rike aikin ofishinka da gaskiya da daraja da kauna na ‘dan-kishin kasa mai son cigaba.”

A daidai wannan lokaci kungiyar gwamnonin Arewacin Najeriya 19 sun fitar da jawabi na musamman ta bakin shugabansu watau gwamna Simon Lalong na jihar Filato.

Shugaban gwamnonin na Arewa ya ce Najeriya ta yi rashi na mutum mai kokari wanda ya kasance ya na taimakawa gwamnatin Buhari da kishi da rikon amana da gaskiya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel