Yanzu nan: Tsohon Ma’aikacin lafiya ya mutu da alamun COVID-19 a Gwoza

Yanzu nan: Tsohon Ma’aikacin lafiya ya mutu da alamun COVID-19 a Gwoza

A jihar Borno, an shiga cikin wani hali a sakamakon mutuwar wani malamin lafiya a garin Gwoza. An samu cutar COVID-19 a jikin wannan tsohon ma'aikaci da ya rasu.

Daily Trust ta rahoto cewa ana zargin cewa wasu alamomin cutar Coronavirus ne su ka kashe wannan malami da ke aiki da wani kamfanin kasar waje da ke aiki a Gwoza.

Jaridar ta ce wani Likita da ke aiki a asibitin koyar da harkar kiwon lafiya na jami’ar Maiduguri watau UMTH, ya tabbatar da cewa lallai Mamacin ya mutu da cutar COVID-19.

Rahotanni sun ce yanzu haka ana feshe gidan Marigayin domin takaita yaduwar wannan cuta. Ana tsoron cewa akwai wadanda su ka kamu da cutar daga jikin Mariagayin.

Majiyar ta shaida cewa wasu malaman lafiya sun yi tarayya da wannan mutumi wanda ya kasance abokin aikinsu kafin ya mutu, kuma akwai yiwuwar ya goga masu cutar.

KU KARANTA: Malamai sun yi addu'a a Jihar Borno bayan rasuwar Abba Kyari

Kafin mutuwar marigayin, ya yi hulda da ma’aikatan asibitin koyon aiki na UMTH, haka zalika ya gana da wasu ma’aikatan na dabam tsakanin Pulka zuwa garin Maiduguri.

“Wasu malaman asibiti biyu ne su ka kawo shi asibitin koyon aikin UMTH ne daga Kauyen Pulka. Su kan su yanzu malaman lafiyar nan su na cikin hadarin kamuwa da cutar.”

Wani daga cikin ‘yan kwamitin da ke yaki da cutar COVID-19 a jihar Borno ya tabbatar da wannan lamari, ya shaidawa ‘yan jarida cewa gwaji ya nuna yanzu sun samu cutar a jihar.

A dalilin haka ne wannan kwamiti ya shirya wani zama na gaggawa a yau Lahadi, 19 ga watan Afrilu domin tattaunawa game da sakamakon gwajin da ya nuna bullar cutar.

Kawo yanzu ba a iya jin ta bakin gwamnati da hukumar NCDC ba. A jiya da dare hukumar NCDC mai takaita yaduwar cututtuka ta ce mutane 542 su ka kamu da cutar a Najeriya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel