Marigayi Kyari ya rike amana, bai kasance Maras gaskiya ba – Garba Shehu

Marigayi Kyari ya rike amana, bai kasance Maras gaskiya ba – Garba Shehu

A lokacin da aka kawo gawar Abba Kyari zuwa Garin Abuja a ranar Asabar, daidaikun mutane ne kurum su ka samu damar yi masa sallar janaza saboda annobar cutar Coronavirus.

Malam Abba Kyari ya cika ne bayan ya yi ‘yar fama da COVID-19 tun karshen watan Maris. Wadanda su ka san Marigayin, sun kwarara masa yabo tare da wanke shi daga zargi.

Mai magana da yawun bakin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Garba Shehu ya bayyana dabi’ar Marigayi Malam Abba Kyari, wanda ta ke akasin abin da wasu mutane ke fada.

Malam Garba Shehu ya ke cewa Abba Kyari ya kasance mutum mai gaskiya da rikon amana. Shi ma Ismaila Isa ya ba Marigayin irin wannan shaida ta kirki bayan an bizne shi a jiya.

Malam Ismail Isa Funtua wanda ya yi aiki da Abba Kyari a gidan jaridarsa ta The Democrats shekarun baya, ya ce Kyari mutum ne mai gaskiya da kuma kokari wajen neman halal.

Ismaila Isa wanda ya na cikin aminan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce: “Mun yi rashi, mun yi rashi.” An ji wannan ne a wani bidiyo da Vanguard ta dauka a ranar Asabar.

KU KARANTA: Abubuwan alheri da jama'a su ke fada bayan Abba Kyari ya cika

Marigayi Kyari ya rike amana, bai kasance Maras gaskiya ba – Garba Shehu

Jama’a ba su fahimce Abba Kyari ba inji Kakakin Shugaba Buhari
Source: Facebook

Garba Shehu ya ke fadawa manema labarai cewa: “Idan ka na neman ‘dan Najeriya daya tal da aka yi wa mummunar fahimta, to wannan mutumi shi ne (Marigayi) Abba Kyari.”

Mai magana a madadin shugaban Najeriyar ya ce game da Kyari: “Ba mutum maras gaskiya ba ne, kuma ya kasance tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari kashi 100 bisa 100.”

“Ya yi duk abin da zai iya a bakin aikinsa, ya na dangantaka da shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ta zarce shekaru 40, saboda haka ya san duk manufofin shugaban kasa.”

“Malam Abba Kyari ya tabbatar ya bi bayan duk wani buri da akidar shugaban kasa Muhammadu Buhari. Mutane da-dama sun yi kokarin karkatar da shi, amma bai bari an saye shi ba.”

Ya ce: “Ya nesanta kansa da Miyagun kasa. Watakila don haka ne wasu ke zargin cewa ya na da girman kai, amma Abba Kyari bai bari wani ya juyasa daga tafarkin shugaban kasa ba.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel