Sabbin mutane 49 sun kamu da cutar covid-19 a Najeriya, 10 daga Kano

Sabbin mutane 49 sun kamu da cutar covid-19 a Najeriya, 10 daga Kano

A daren ranar Asabar ne hukumar yaki da cututtuka ma su yaduwa a kasa (NCDC) ta sanar da samun karin sabbin mutane 49 da suka kamu da kwayar cutar covid-19 a fadin Najeriya.

A cikin sanarwar da ta fitar a shafinta na tuwita, NCDC ta ce an samu karin sabbin mutane 23 da suka kamu da kwayar cutar Legas, 12 a Abuja da karin wasu 10 daga jihar Kano.

Sauran jihohin da aka tabbatar da samun ma su dauke da kwayar cutar sun hada da jihar Ogun; mutum biyu, sai jihar Oyo da jihar Ekiti ma su mutum daya kowannensu.

Samun karin mutanen 49 a ranar Asabar ya mayar da jimillar ma su dauke da kwayar cutar a fadin Najeriya zuwa 542.

An sallami jimillar mutane 166 daga cibiyoyin killacewa da ke fadin kasar nan bayan an tabbatar da warkewarsu.

Ya zuwa yanzu annobar cutar covid-19 ta hallaka mutane 19 a Najeriya, cikinsu har da shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, marigayi Abba Kyari.

Farfesa Akin Abayomi, kwamishinan lafiya a jihar Legas, ya ce marigayi Abba Kyari, tsohon shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, ya mutu ne a wani asibitin kwararru da ake duba ma su ciwon zuciya.

DUBA WANNAN: An hana wasu hadiman Buhari shiga fadar shugaban kasa bayan sun halarci jana'izar Abba Kyari

A wata ganawa da ya taba yi da manema labarai a baya, kwamishinan ya bayyana cewa bashi da masaniyar inda aka kai marigayin yayin da ya dawo Legas bayan an tabbatar da cewa ya na dauke da kwayar cutar covid-19.

A cikin wani jawabi da ya fitar ranar Asabar a shafinsa na Tuwita domin amsa tambayoyi a kan mutuwar Kyari, Farfesa Abayomi ya ce asibitin da aka kwantar da Kyari ya samu sahalewar hukuma domin duba ma su cutar covid-19.

A ranar Juma'a ne ministan lafiya, Dakta Osagie Ehanire, ya bayyana cewa ya zuwa yanzu babu wani asibiti mai zaman kansa da aka bawa lasisi ko izinin duba ma su fama da cutar covid-19.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel