Kwamishinan lafiya a jihar Legas ya yi karin bayani a kan mutuwar Abba Kyari
Farfesa Akin Abayomi, kwamishinan lafiya a jihar Legas, ya ce marigayi Abba Kyari, tsohon shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, ya mutu ne a wani asibitin kwararru da ake duba ma su ciwon zuciya.
A wata ganawa da ya taba yi da manema labarai a baya, kwamishinan ya bayyana cewa bashi da masaniyar inda aka kai marigayin yayin da ya dawo Legas bayan an tabbatar da cewa ya na dauke da kwayar cutar covid-19.
A ranar Juma'a ne fadar shugaban kasa ta sanar da mutuwar Kyari, an binne shi ranar Asabar bisa tsarin addinin Musulunci.
A cikin wani jawabi da ya fitar ranar Asabar a shafinsa na Tuwita domin amsa tambayoyi a kan mutuwar Kyari, Farfesa Abayomi ya ce asibitin da aka kwantar da Kyari ya samu sahalewar hukuma domin duba ma su cutar covid-19
"Malam Abba Kyari ya mutu ne a asibitin 'First Cardiology Consultants' da ke Legas sakamakon kamuwa da cutar covid-19.
"Asibitin ya na daga cikin manyan asibitoci na zamani da ma'aikatar lafiya ta jiha ta bawa damar duba ma su dauke da kwayar cutar covid-19.
"Asibitin ya ware wani sashe na musamman domin duba lafiyar wadanda ke son zuwa asibitin domin ake dubasu bayan an tabbatar su na dauke da kwayar cutar covid-19.
DUBA WANNAN: Manyan annoba 6 da aka taba yi a duniya da adadin mutanen da kowacce ta hallaka
"Mahukuntan asibitin su na bawa hukuma hadin kai tare da tuntubar kwamitin ko ta kwana a kan annobar covid-19 na jihar Legas wajen gudanar da aiyukansu," a cewar Farfesa Abayomi.
A ranar Juma'a ne ministan lafiya, Dakta Osagie Ehanire, ya bayyana cewa ya zuwa yanzu babu wani asibiti mai zaman kansa da aka bawa lasisi ko izinin duba ma su fama da cutar covid-19.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng