Buhari ya yi ta’aziyyar mutuwar Uwargidar sarkin Daura da tsohon kwamishinan shari’a na Kano

Buhari ya yi ta’aziyyar mutuwar Uwargidar sarkin Daura da tsohon kwamishinan shari’a na Kano

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya mika ta’aziyya ga Sarkin Daura, Alhaji Umar Farouk Usman, a kan mutuwar uwargidarsa, Hajiya Binta Umar

- Buhari ya kuma taya gwamnati da mutanen jahar Kano alhinin mutuwar tsohon Atoni-Janar kuma kwamishinan shari’a na jahar, Alhaji Aliyu Umar

- Ya yi addu'an Allah ya ji kan mamatan tare da ba iyalansu hakuri da juriyar rashin da suka yi

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya mika ta’aziyya ga Sarkin Daura, Alhaji Umar Farouk Usman, a kan mutuwar uwargidarsa, Hajiya Binta Umar.

Malam Garba Shehu, babban mai ba shugaban kasa shawara a kafofin watsa labarai a wani jawabi da ya saki a ranar Juma’a, 17 ga watan Afrilu, ya ce shugaban kasar, wanda ya kira sarkin a waya ya ce:

“Zuciyata ta tabu sosai sannan na yi bakin ciki da mutuwar uwargidarka Hajiya Binta Umar a shekara 70.

“Marigayiyar ta yi rayuwa mai inganci da ya cancanci ayi koyi da ita. Ta kasance nagartacciya.

“Zuciyana da addu’o’i na tare da ahlin ka a kan mutuwar wannan ginshiki na gidanka.”

Buhari ya yi ta’aziyyar mutuwar Uwargidar sarkin Daura da tsohon kwamishinan shari’a na Kano
Buhari ya yi ta’aziyyar mutuwar Uwargidar sarkin Daura da tsohon kwamishinan shari’a na Kano
Asali: Depositphotos

Shugaba Buhari ya yi addu’ar Allah ya ji kan Hajiya Binta sannan ya saka mata da gidan aljannah.

Ya kuma yi addu’an Allah ya ba sarkin da ahlinsa juriyar wannan rashi da suka yi.

Hakazalika Shugaban kasa Buhari ya taya gwamnati da mutanen jahar Kano alhinin mutuwar tsohon Atoni-Janar kuma kwamishinan shari’a na jahar, Alhaji Aliyu Umar.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: An sake samun mutum 2 dauke da Covid-19 a Katsina

Shugaban kasar ya jadadda sadaukarwa da jajircewar da Aliyu ya yi wajen inganta bangaren shari’a a kasar.

Shugaban kasar ya yi ta’aziyya ga iyalan hazikin lauyan, kungiyar lauyoyin Najeriya da kuma abokan aikinsa.

Ya ce marigayin ya sadaukar da rayuwarsa wajen yiwa kasar da al’umma hidima.

Ya yi addu’an Allah ya ji kan mamacin sannan kuma ya ba iyalansa juriyar rashin sa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel