Coronavirus: An sauke gwamnan da ya dage sai an yi sallar jam'i a kasar Sudan

Coronavirus: An sauke gwamnan da ya dage sai an yi sallar jam'i a kasar Sudan

- Firai Ministan kasar Sudan, Abdalla Hamdok, ya tsige gwamnan Khartoum, babban birnin kasar

- Hakan ya biyo bayan kin dokar hana yin sallar jam'i wanda gwamnati ta kafa, a kokarinta na hana yaduwar cutar coronavirus

- Zuwa yanzu an tabbatar mutane 32 da ke dauke da COVID-19 a Sudan, inda mutane biyar suka mutu, sannan mutane hudu suka warke

Firai Ministan kasar Sudan, Abdalla Hamdok, ya tsige gwamnan Khartoum, babban birnin kasar, bayan ya nuna tirjiya a kan dokar hana yin sallar jam'i wanda gwamnati ta kafa.

Hakan ya kasance daga cikin kokarin da gwamnatin Sudan ke yi na hana yaduwar annobar coronavirus.

Sai dai Janar Ahmed Abdun Hammad Mohammed ya ki aiwatar da matakin da aka dauka, na haramta yin sallah a masallatai da kuma ibada a cocina wacce za ta soma aiki a ranar Asabar.

An tattaro cewa, zuwa safiyar ranar Juma'a, 17 ga watan Afrilu, an tabbatar mutane 32 da ke dauke da COVID-19 a Sudan, inda mutane biyar suka mutu, sannan mutane hudu suka warke.

Coronavirus: An sauke gwamnan da ya dage sai an yi sallar jam'i a kasar Sudan

Coronavirus: An sauke gwamnan da ya dage sai an yi sallar jam'i a kasar Sudan
Source: Twitter

Tun da farko, a ranar Alhamis 'yan sanda suka fesa barkonon-tsohuwa kan masu goyon bayan hambararren shugaban kasar Omar al-Bashir, shashin Hausa na BBC ta ruwaito.

Sun yi zanga-zangar ne domin adawa da matakin da gwamnatin rikon kwarya ta dauka na aiwatar da shirin tsuke bakin aljihun gwamnati.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya ta fara rabon kayan rage radadin COVID-19 ga gidaje 600,000 a Abuja

A wani labarin, mun ji cewa kasashen duniya da dama sun saka dokoki daban-daban don takaita yaduwar annobar.

Kasar Saudi Arabia da Jordan sun dakatar da sallar Taraweeh a masallatai.

Ma'aikatar al'amuran addini, Da'awah da kuma shiriya ta kasar Saudi ta ce kowa yayi sallar taraweeh a gida a watan Ramadan don za a rufe dukkan masallatan kasar har sai annobar ta kare.

Hakazalika, kasar Misra ba a barta a baya ba. Ta bayyana cewa masallatan kasar za su kasance a rufe har sai babu wani mai cutar a kasar.

Kasar Malaysia ta bayyana cewa babu taron buda baki a kasar kwata-kwata. Gwamnatin kasar Malaysia ta ce ba za ta lamunci taron buda baki ba a watan Ramadan.

A UAE kuwa, duk masu bada sadakar kayan buda baki ko abinci za su kai ne har gida. Babu wani tanti ko taro da za a hada don rabon kayan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel