Gwamnatin tarayya ta fara rabon kayan rage radadin COVID-19 ga gidaje 600,000 a Abuja

Gwamnatin tarayya ta fara rabon kayan rage radadin COVID-19 ga gidaje 600,000 a Abuja

- Gwamnatin taraya ta fara rabon kayan rage radadin COVID-19 ga talakawa a babbar birnin tarayya Abuja

- Karamar ministar birnin tarayya, Ramatu Aliyu, ce ta kaddamar da rabon kayayyakin a ranar Juma’a, 17 ga watan Afrilu

- An fara rabon ne daga yankin Abaji da ke birnin tarayyar kasar

Gwamnatin tarayya ta fara rabon kayayyakin tallafin COVID-19 ga gidaje 600,000 a babbar birnin tarayya Abuja.

Karamar ministar birnin tarayya, Ramatu Aliyu, ce ta kaddamar da rabon kayayyakin a ranar Juma’a, 17 ga watan Afrilu.

Hakan na daga cikin kokarin da gwamnati ke yi domin ganin ta rage ma mutane radadin da annobar COVID-19 wacce aka fi sani da coronavirus ta kawo a kasar.

Daga cikin mutane 442 da aka tabbatar suna da COVID-19, mutane 13 ciki harda wani likita sun mutu, yayinda marasa lafiya 152 suka warke daga cutar.

Ministar ta bayar da tabbacin cewa talakawa da marasa gata a birnin tarayya za su amfana daga shirin tallafin.

A bisa ga rubutun da hukumar birnin tarayyar ta wallafa a shafinta na Twitter, an fara rabon ne daga yankin Abaji da ke Abuja.

Ta wallafa: " Karamar ministar FCT, @DrRamatuAliyu a safiyar yau za ta kaddamar da rabon kayayyakin tallafi domin rage wa mutane radadin #COVID19 a FCT, za a fara daga yankin Abaji, #COVID19FCT."

KU KARANTA KUMA: Makonni hudu bayan kwantar dashi: Har yanzu dan Atiku Abubakar na dauke da cutar COVID-19

A gefe guda mun ji cewa, kusoshin gwamnati a Najeriya sun fara tumke damarar rarraba hasken lantarki ga 'yan kasar kyauta har na tsawon watanni biyu.

Gwamnatin kasar ta kudiri aniyyar hakan ne domin saukakawa al'umma matsin rayuwa da za su fuskanta a yayin da annobar coronavirus ta yi sanadiyar tilastawa 'yan kasar zaman gida.

A yunkurin haka gwamnati tare da sauran masu ruwa da tsaki ta gudanar da wani taro dangane da yadda za a bullowa lamarin na tabbatar da an wadata al'umma da hasken lantarki.

Wakilai daga majalisar tarayya da kuma masu ruwa da tsaki a fannin lantarki sun gudanar da taron ne a ranar Alhamis.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel