Yanzu Yanzu: Allah ya yiwa tsohon Atoni-Janar na Kano, Aliyu Umar rasuwa

Yanzu Yanzu: Allah ya yiwa tsohon Atoni-Janar na Kano, Aliyu Umar rasuwa

- Tsohon Atoni Janar kuma kwamishinan shari’a na jahar Kano, Aliyu Umar, ya rasu

- Marigayin ya rasu ne a safiyar ranar Juma’a, 17 ga watan Afrilu, da misalin karfe 4:00 na asuba bayan yar gajeriyar rashin lafiya

- Tuni aka binne shi, daidai da koyarwar addinin Islama

Allah ya yiwa tsohon Atoni Janar kuma kwamishinan shari’a na jahar Kano, Aliyu Umar, rasuwa.

Ya rasu ne a safiyar ranar Juma’a, 17 ga watan Afrilu, da misalin karfe 4:00 na asuba bayan yar gajeriyar rashin lafiya.

Yanzu Yanzu: Allah ya yiwa tsohon Atoni-Janar na Kano, Aliyu Umar rasuwa
Yanzu Yanzu: Allah ya yiwa tsohon Atoni-Janar na Kano, Aliyu Umar rasuwa
Asali: UGC

Tuni aka binne shi, daidai da koyarwar addinin Islama.

Marigayi Aliyu Umar ya kasance kwararren lauya mara tsoro, kuma daya daga cikin hazikai a Najeriya.

KU KARANTA KUMA: A binciki abin da ya sabbaba gobara a sansanin yan gudun hijira dake Ngala – Buhari

A wani labari na daban, mun ji cewa gidauniyar Bill and Melinda Gates ta bayyana cewa yankin Arewacin Najeriya ta fi ko ina kasancewa cikin hadarin fuskantar yaduwar annobar Coronavirus.

Shugaban gidauniyar, Mark Susman ya bayyana haka ga yan jaridu a ranar Alhamis, inda yace Arewa na cikin hadarin saboda rashin sahihin tsarin kiwon lafiya a matakin farko.

“Mun yi aiki sosai a yankin Arewa saboda shi ne yanki mafi talauci a Najeriya, tsarin kiwon lafiya a yankin ya tabarbare gaba daya, shi yasa mata masu haihuwa da kananan yara suka fi mutuwa a yankin.

“Kasashen Afirka da dama suna da irin wannan matsalar, don haka muke ganin matsalar rashin tsarin ingantaccen kiwon lafiya a matakin farko zai zamo hanya mafi sauki da zai sanya yankin cikin hadarin yaduwar cutar.” Inji shi.

Har ila yau, Hukumar lafiya ta duniya, WHO ta nemi kasashen dake kokarin janye dokar ta bacin da suka sanya don gudun kare yaduwar annobar Coronavirus su cika sharudda guda 7.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito shugaban WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ne ya bayyana haka a ranar Alhamis yayin da yake ganawa da manema labaru.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng