Ahmaad ya fallasa bidiyon bogin da Sanata Melaye ya wallafa a Tuwita

Ahmaad ya fallasa bidiyon bogin da Sanata Melaye ya wallafa a Tuwita

Gwamnatin tarayya ta tsawaita wa’adin zaman kulle wanda ake kukan hakan ya jefa mutane cikin halin ha’ula’i. Sai dai hakan ne zai taimaka wajen rage yaduwar cutar COVID-19.

Sanata Dino Melaye ya fito shafinsa na sada zumunta ya yada wani bidiyo inda ya yi ikirarin cewa cincirondon jama’a ne su ke wasoso yayin da gwamnati ke raba tallafin kayan abinci.

An ga wannan bidiyo a shafin Dino Melaye na Tuwita a yau Alhamis 16 ga watan Afrilu, 2020 da kimanin karfe 12:30 na rana. Sama da mutum 60, 000 sun kalli wannan gajeren bidiyo.

Jim kadan bayan wannan bidiyo ya shiga gari sai wani daga cikin hadiman shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya fito ya fadawa jama’a gaskiyar lamarin, ya karyata ‘dan siyasar.

Bashir Ahmaad ya nuna cewa an dauki wannan bidiyo ne a shekarar bara. Hadimin shugaban Najeriyar ya ce tsohon Sanatan ya yada bidiyon ne domin ya tadawa Bayin Allah hankali.

Ahmaad wanda ya ke taimakawa shugaba na Najeriya kan harkokin da su ka shafi kafafen sada zumuntan zamani ya tambayi Sanatan ko ya na jin dadin halin da annoba ta jefa jama’a.

KU KARANTA: Buhari ya aikawa Firiyim Ministan Ingila wasika bayan ya warke

Hadimin shugaban kasar ya bankado karyar ‘dan adawar ne kusan sa’a uku bayan ya wallafa bidiyon. Ahmaad ya ce kamata ya yi ace Melaye ya tantance bidiyon kafin ya yada shi.

Ga abin da Ahmaad ya fadawa Melaye:

“Sanata Dino Melaye, tsohon ‘dan majalisar dattawan Najeriya wanda ya ke da mabiya fiye da miliyan guda ya na yada labarin bogi, na tsohon bidiyon da aka dauka a bara domin ya dada tada hankalin jama’a a lokacin da ‘Yan Najeriya su ke cikin halin dar-dar na wayyo Allah.”

Matashin ya tambayi Dino Melaye wanda ya ke da mabiya kusan miliyan daya da rabi a shafin Tuwita ko halin da ake ciki ya na yi masa dadi. Har yanzu Sanatan bai cire bidiyon ba.

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa an fara fitowa da wannan bidiyo ne a lokacin da jam’iyyar APC ta ke yakin neman zaben gwamna a jihar Legas a 2019 inda ‘dan takararta ya raba shinkafa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng News

Online view pixel