'Yan bindiga sun sace ma su jego uku a Kaduna

'Yan bindiga sun sace ma su jego uku a Kaduna

- 'Yan bindiga sun yi awon gaba da wasu mata ma su jego guda uku a karamar hukumar Giwa a jihar Kaduna

- 'Yan bindigar sun yi yunkurin tafiya da mata 13 ne da farko, amma sai jama'ar gari su ka tunkaresu

- Wani mazaunin kauyen ya ce dokar kulle ta jefa rayuwar 'yan bindiga cikin mawuyacin halin rashin abinci

Wasu 'yan bindiga sun yi awon gaba da mata ma su jego guda uku a kauyen Karaukarau da ke karamar hukumar Giwa a jihar Kaduna.

Wani mazaunin kauyen mai suna Malam Sani Bakali ya shaidawa wakilin jaridar 'The Nation' cewa 'yan bindigar, dauke da muggan makamai, sun fara yunkurin tafiya da mata 13 daga kauyen.

Ya kara da cewa mazauna kauyen sun cire tsoro, sun tunkari 'yan bindigar tare da hanasu tafiya da dukkan matan 13.

Bakali ya bayyana cewa, 'yan bindigar da su ka dira a kauyen ranar Talata, sun yi awon gaba da ma su jegon yayin da ake wani bikin aure.

"Dokar kulle ta jefa 'yan bindiga a cikin mawuyacin halin rashin abinci, lamarin da ya sa su ke kai farmaki wuraren bikin aure a kauyuka.

'Yan bindiga sun sace ma su jego uku a Kaduna

'Yan bindiga sun sace ma su jego uku a Kaduna
Source: Twitter

"Sun zo kauyenmu ranar Talata tare da yunkurin sace wasu mata 13 a wurin wani biki," a cewar Bakali

Ya bayyana cewa mazauna kauyen sun tunkari 'yan bindigar bayan sun samu labarin abin da ke faruwa, inda su ka tserar da 10 daga cikin matan, yayin da 'yan bindigar su ka yi awon gaba da ma su jegon, su uku.

DUBA WANNAN: An harbi mutum daya yayin da mata da matasa su ka fito zanga-zangar hana fita a Delta

Babu labarin cewa 'yan bindigar sun saki ma su jegon har zuwa lokacin wallafa wannan rahoto.

A cewar Bakali, sun sanar da babban rundunar ofishin 'yan sanda na karamar hukumar Giwa afkuwar lamarin.

Amma da aka tuntubi kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige, ya ce, ya zuwa wannan lokaci maganar ba ta zo kan teburinsa ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel