Jami'an tsaro sun kashe mutane 18 yayin tabbatar da dokar zaman gida a Najeriya - NHRC

Jami'an tsaro sun kashe mutane 18 yayin tabbatar da dokar zaman gida a Najeriya - NHRC

Hukumar kare hakkin bil'adama ta kasa (NHRC) ta ce jami'an tsaro sun kashe mutane 18 yayin kokarin tabbatar da jama'a sun zauna a gida don dakile yaduwar annobar cutar coronavirus da ke cigaba da shiga jihohin kasa.

Najeriya, kasar nahiyar Afrika ma fi yawan jama'a, ta saka dokar rufe rufe manyan biranenta; Legas da Abuja, tare da saka dokar takaita zirga-zirga a sauran sassan kasar domin dakile yaduwar annobar covid-19.

A cewar alkaluman hukuma, mutane 407 sun kamu da cutar covid-19 a jihohi fiye da 20.

An baza jami'an tsaro da suka hada da 'yan sanda da sojoji domin tabbatar da cewa jama'a sun yi biyayya ga dokar zaman gida da hukuma ta saka.

A wani rahoto da NHRC ta fitar ranar Laraba, ta bayyana cewa, "mun samu korafi 105 a kan take hakkin bil'adama da jami'an tsaro su ka yi a jihohi 24.

"Daga cikin korafin, akwai kisan gilla da aka yi wa mutane 8, lamarin da ya kawo jimillar mutanen da aka kashe zuwa 18," a cewar NHRC.

Jami'an tsaro sun kashe mutane 18 yayin tabbatar da dokar zaman gida a Najeriya - NHRC

Jami'an tsaro sun kashe mutane 18 yayin tabbatar da dokar zaman gida a Najeriya - NHRC
Source: Depositphotos

NHRC ta ce adadin mutanen da jami'an tsaro su ka kashe sun fi yawan wadanda annobar covid-19 ta hallaka.

"A yayin da cutar covid-19 ta kashe mutane 11 a fadin kasa, jami'an tsaro sun kashe mutane 18 yayin tabbatar da dokar zaman gida," a cewar rahoton NHRC na ranar Laraba.

DUBA WANNAN: Tinubu ya shawarci FG ta yi amfani da BVN wajen bawa 'yan Najeriya tallafin jin kai

Hukumar ta zargi jami'an tsaro da amfani da karfi a kan fararen hula, amfani da iko ta hanyar da bai dace ba, cin hanci, da saba ka'idojin aikin tsaro na Najeriya da kasa da kasa.

Sai dai, kakakin rundunar 'yan sanda na kasa, Frank Mba, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, "NHRC bugu ta ke yi ba kama suna a cikin zarginta.

"Ya kamata hukumar NHRC ta fitar da bayanai a kan mutanen da aka kashe, kuma ya kamata ta bayar da cikakken bayani a kan jami'an tsaron wacce hukuma ne su ka kashe mutanen, kuma a ina."

Mba ya bayyana cewa rundunar 'yan sanda za ta cigaba da aikinta na tabbbatar da doka bisa tsarin dokokin aiki da na kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel