Coronavirus: Malamai sun amince da dakatar da sallar Juma'a a Kano

Coronavirus: Malamai sun amince da dakatar da sallar Juma'a a Kano

Gamayyar malamai a jahar Kano, sun amince da dakatar da sallar juma’a a fadin masallatan jahar, a yayin da dokar hana fita da gwamnati ta saka ke fara aiki a yau Alhamis, 16 ga watan Afrilu.

Shashin Hausa na BBC ta ruwaito cewa Malaman sun gudanar da wata taro kan haka a Africa House da ke fadar gwamnatin Kano a yau Alhamis.

Dokar da gwamnatin jahar ta sanya na hana fita zai fara aiki ne a yau kuma zai shafe tsawon mako guda.

Hakan na daga cikin kokarin da gwamnatin ke yi na hana yaduwar cutar coronavirus wacce ta shiga jahar a ranar Asabar da ta gabata.

Coronavirus: Malamai sun yarda da dakatar da sallar Juma'a a Kano

Coronavirus: Malamai sun yarda da dakatar da sallar Juma'a a Kano
Source: Depositphotos

Shawarwarin malaman dai na zuwa ne bayan da hukumomi a Kano suka sanar da mutuwar wani mutum mai dauke da cutar COVID-19 a jahar. Sannan adadin wadanda suka kamu da cutar ya kai mutum 21.

Majiyar tamu ta tattaro cewa Malaman sun yi nazarin harkokin rayuwar al'umma ne wadanda ke da nasaba da taron jama'a da nufin bayar da fatawa, inda suka yarda da dakatar da Sallar Juma'a a masallatan jahar.

Sakataren kwamitin malamai da kwamitin kar ta kwana na coronavirus , Dr. Ibrahim Mu’azzam mai Bushira, ya ce malaman sun amince da a dakatar da gabatar da Sallar Juma’a don gudun kada wani da ke dauke da cutar ya yada ta a tsakanin al’umma.

KU KARANTA KUMA: Sakamakon gwajin mutane 90 da ke nuna alamun COVID-19 a Abuja ya fito, basa dauke da cutar

A baya mun ji cewa, ma'aikatar lafiya a jihar Kano ta sanar da mutuwar mutum na farko da aka tabbatar da cewa ya na dauke da kwayar cutar covid-19.

Ma'aikatar lafiyar ta sanar da hakan ne a cikin wani takaitaccen sako da ta wallafa a shafinta na Tuwita a daren ranar Alhamis.

Duk da ma'aikatar ba ta bayar da karin bayani a kan mai dauke da cutar da ya mutu ba, ta tabbatar da cewa yanzu haka akwai jimillar mutane 21 da su ka kamu da cutar a jihar, sabanin mutum 16 da NCDC ta bayyana.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel