Gaskiyar dalilin da ya sa IMF ta cire Najeriya cikin kasashe 25 da ta yiwa sassauci – Ministar kudi

Gaskiyar dalilin da ya sa IMF ta cire Najeriya cikin kasashe 25 da ta yiwa sassauci – Ministar kudi

Ministar kudi ta Najeriya, Zainab Shamsuna Ahmed ta bayyana ainahin dalilin da ya sa Asusun Lamuni na Duniya wato IMF ba ta sanya Najeriya cikin kasashe matalauta da za'a yi wa sassaucin biyan bashi ba.

A makon nan ne dai IMF ta ce zata jinkirta wa matalautan kasashe 25 biyan bashin da take bin su zuwa wata shida domin su yi amfani da kudin wajen yaki da cutar coronavirus.

Daga cikin kasashen akwai Jamhuriyar Nijar da kasar Congo DRC.

Sai dai rashin kasancewar Najeriya a cikin kasashen, ya sa wasu tambayar dalilin faruwar hakan.

Don haka ministar kudin, ta fayyace biri har witsiya, cewa Najeriya bata samu sassaucin bashi daga IMF ba ne saboda ba bu bashin da ake binta.

Gaskiyar dalilin da ya sa IMN ta cire Najeriya cikin kasashe 25 da ta yi wa sassauci – Ministar kudi
Gaskiyar dalilin da ya sa IMN ta cire Najeriya cikin kasashe 25 da ta yi wa sassauci – Ministar kudi
Asali: UGC

A sakon da ta wallafa a Twitter ranar Alhamis, 16 ga watan Afrilu, ministar ta ce tun da IMF ba ta bin Najeriya bashi, babu bukatar ta yafe mata shi.

Ta wallafa cewa: “Tun da asusun IMF ba ta bin Najeriya bashi, babu wani bashi da ke kasa da za a yafe mata. “

“Ana cikin nazari kan sabon bashin da Najeriya ta nema daga IMF kuma yana samun kulawa. Sabon bashin da ta nema yana karkashin shirin kudin gaggawa wato Rapid Financing Initiative (RFI).“

"Najeriya na da damar karbar kaso 100 na bukatarta a karkashin shirin RFI. Matakin kudinmu a IMF a yanzu a bayyane yake a shafin IMF na yanar gizo."

KU KARANTA KUMA: Sai kowace jaha a Najeriya ta samu rabonta na coronavirus – Shugaban NCDC

A wani labarin, mun ji cewa gwamnatin tarayya ta bayar da sahalewarta a kan biyan N200bn domin bunkasa samuwar makamashi na iskar gas ga kamfanoni masu rarraba wutar lantarki.

Daily Trust ta ruwaito cewa, gwamnati ta malalo wannan makudan kudi domin bunkasa samun wutar lantarki a kasar yayin da annobar covid-19 ta yi sanadiyar tilastawa al'umma zaman gida.

Shugaban kamfanin man fetur na kasa NNPC, Mallam Mele Kyari, shi ne ya bayar da shaidar hakan yayin ganawa da manema labarai a ranar Laraba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel