Tallafi 17 da Gwamnatin tarayya ta samu domin yaki da cutar COVID-19

Tallafi 17 da Gwamnatin tarayya ta samu domin yaki da cutar COVID-19

Kasar Najeriya na ci gaba da gwagwarmaya domin ganin ta shawo kan annobar coronavirus wacce ta addabi duniya baki daya.

Hakan ya sanya manyan masu kudi da kasashe masu karfi ke ta tururruwan kawo nasu gudunmawar wanda suka hada da kudade, kayayyakin agaji, kayan asibiti da sauransu.

Legit.ng ta yi amfani da wannan damar wajen zakulo maku tarin tallafi da gwamnatin tarayya ta samu daga manyan attajirai da kungiyoyi masu zaman kansu.

Tallafi 17 da Gwamnatin tarayya ta samu domin yaki da cutar COVID-19
Tallafi 17 da Gwamnatin tarayya ta samu domin yaki da cutar COVID-19
Asali: Twitter

Ga su nan kamar haka:

1. Kungiyar tarayyar Turai (EU)

Kungiyar hadakar kasashen nahiyar Turai (EU) ta bawa Najeriya tallafin Yuro miliyan hamsin (£50m) domin yaki da annobar cutar covid-19.

Shugaban tawagar wakilan EU, Ambasada Ketil Karlsen, ne ya sanar da hakan yayin ziyarar da suka kai wa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a fadarsa ranar Talata.

Yawan kudin ya kai biliyan N21 idan aka juya shi zuwa kudin Najeriya.

2. Majalisar dikin Duniya

A ranar Talata, 14 ga Watan Afrilu, gwamnatin Najeriya ta karbi wasu kayan asibiti da majalisar dinkin Duniya ta aiko da su kasar domin yakar annobar cutar COVID-19.

Ministan harkokin jirgin sama, Hadi Sirika da wasu daga cikin ‘yan kwamitin da shugaban kasa ya kafa domin yaki da cutar COVID-19 a Najeriya ne su ka karbi wadannan tarin kaya.

Daga cikin wadannan kayan asibiti da aka kawo akwai na’urorin taimakawa numfashi watau ‘Ventilators’ na samfurin A30 guda 50 da kuma wasu rigunan kare-kai na Malaman asibiti.

3. Gidauniyar Jack Ma

Gidauniyar wani attajiri dan kasar China, Jack Ma Foundation, ta bawa Najeriya tallafin kayan kiwon lafiya domin yakar annobar cutar coronavirus.

Kayan tallafin sun hada da wasu akwatuna 107 da ke cike da kayan duba lafiya da suka hada da kayan tiyata, kayan gano kwayar cutar corona, kayan ma'aikatan lafiya da ke duba marasa lafiya da sauransu.

4. China Civil Engineering Construction Corporation (CCECC)

Kamfanin gine-gine ta kasar China wato China Civil Engineering Construction Corporation (CCECC) ma ta aiko da takunkumin fuska guda miliyan daya zuwa Najeriya, a matsayin nata gudunmawar yaki da COVID-19.

Sauran gudunmawar da suka bayar sun hada da na’urorin taimakawa numfashi watau ‘Ventilators’, likitoci daga kasar China da kuma sauran kayayyakin kariya.

5. Ministocin Najeriya

Ministocin kasar ma sun sadaukar da kashi 50 cikin 100 na albashinsu na watan Maris domin taimakawa gwamnatin tarayya wajen yakar Coronavirus.

6. Aliko Dangote

Da farkon shigowar annobar Najeriya, shugaban gidauniyar Dangote, Aliko Dangote ya bayar da gudummawar naira miliyan 200 ga gwamnatin a madadin gidauniyarsa.

Dangote ya zo ya kara kudin zuwa naira biliyan daya sannan ya hada hannu da wani babban banki wajen samar da cibiyar kula da killace masu cutar.

Ya kuma bayar da gudummawar motocin daukar marasa lafiya ga gwamnatin jahar Legas.

7. Femi Otedola

Biloniyan Najeriya, Femi Otedola ma ya ba gwamnati gudummawar naira biliyan daya domin yakar cutar ta Covid-19.

8. Tony Elumelu

A madadin bankin United Bank of Africa (UBA), Tony Elumelu, ya bayar da naira biliyan biyar ga gwamnatin tarayya da wasu jihohin tarayya.

9. Abdulsamad Rabiu

Shugaban kamfanin BUA, Abdulsamad Rabiu ma ya sanar da bayar da kyautar naira biliyan daya ga gwamnati a matsayin gudunmawarsa na yakar cutar ta coronavirus.

10. Modupe da Folorunasho Alakija

Shugaba da mataimakiyar Shugabar Famfa Oil Limited sun bayar da tallafin naira biliyan daya.

11. Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ma ya bayar da naira miliyan 50 a matsayin nasa gudunmawar.

KU KARANTA KUMA: COVID-19: Ana zargin mutane 170 na dauke da coronavirus a Sokoto

12. Asiwaju Bola Tinubu

Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Tinubu ya sanar da bayar da naira miliyan 200 a matsayin nasa gudunmawar a kokarin da gwamnati ke yi a yaki da cutar COVID-19.

13. Herbert Wigwe

Shugaban bankin Access ya bayar da tallafin naira biliyan daya.

14. Segun Agbaje

Manajan darakta na bankin Guaranty Trust Bank GTB ma ya bayar da naira biliyan daya a madadin bankin.

15. Mike Adenuga

Mike Adenuga, wanda shima biloniyan Najeriya kuma mammalakin kamfanin sadarwan Glo ne ya bayar da naira biliyan 1.5.

16. Sanatoci

Mambobin majalisar dattawan Najeriya ma sun bayar da gudunmuwar rabin albashinsu tun daga watan Maris har zuwa lokacin da za a kammala yakar cutar coronavirus.

17. Yan majalisar wakilai

Mambobin majalisar wakilai ma a nasu bangaren sun sadaukar da albashinsu na watanni biyu domin yaki da COVID-19.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel