Covid-19: Nau'ikan abinci masu bunkasa garkuwar jiki

Covid-19: Nau'ikan abinci masu bunkasa garkuwar jiki

A yayin da cutar coronavirus ta zamto ruwan dare a fadin duniya, wasu masana kimiyya a kasar Australia sun ce sun gano yadda garkuwar jiki ke tasiri wajen yakar cutar.

BBC Hausa ta ruwaito masanan sun wallafa sakamakon bincikensu a wata mujallar kimiyya ta Nature Medicine a ranar Talata, 17 ga watan Maris, 2020.

Binciken ya nuna cewa mutane su na warkewa daga coronavirus kamar yadda ake samun waraka daga cuta ta mura.

A cewar masanan, sun gano kwayar halittar da ke zame wa mutum garkuwar jiki kuma hakan yana tasiri wajen samar da riga-kafin cutar coronavirus.

Yayin da mutane da dama suka warke daga coronavirus, masanan sun ce hakan na nufin garkuwar jiki za ta iya yakar cutar duba da yadda ya zuwa yanzu ba a samu maganinta ba.

Kwayar cutar coronavirus
Kwayar cutar coronavirus
Asali: Twitter

Legit.ng ta zakulo wasu nau'ikan abinci masu bunkasa garkuwar jiki, wanda babu shakka masu ta'ammali da su za su ci moriya wajen samun riga-kafin covid-19.

A wannan lokaci da annobar covid-19 ta dugunzuma al'ummar duniya baki daya, baya ga kula da tsaftar jiki da muhalli, akwai kuma bukatar lura da irin abincin da ya kamata a ribata.

Ga jerin wasu nau'ikan abinci da na sha da suka kunshi sunadarai masu albarkar bunkasa garkuwar jiki kamar haka:

Dangin kayan lemu: (Lemun zaki, Lemun tsami, Lemun Taba, Tanjirin, Inibi)

Dangin kayan lemu wanda a turance ake kira da Citrus Fruits, sun kunshi sunadarin Vitamin C, wanda yake taimaka wa jinin mutum bunkasa garkuwa ta yakar cututtuka.

Tattasai:

Jan tattasai ya kunshi sunadaran Vitamin C da kuma Betacarotene wadanda baya ga inganta lafiyar fata, suna kuma bunkasar garkuwar jikin dan Adam.

Tafarnuwa:

Bayan karin dandano ga abinci, tafarnuwa tana tasiri wajen bunkasa garkuwar jiki ta hanyar hana kamuwa da cutar hawan jini.

Citta:

Citta na da nasabar gaske wajen magance cututtukan da suka shafi mura, ta hanyar tsarkake kafofin shakar numfashi musamman makoshi. Tana kuma taimaka wa masu yawan tashin zuciya.

Alayyahu:

Tamkar Jan tattasai, alayyahu ya kunshi sunadaran vitamin C da kuma Betacarotene, masu taka rawar gani wajen bunkasa garkuwar jiki da zai yaki cututtuka.

Madarar shanu:

Vitamin D shi ne babban sunadarin da madarar shanu ta kunsa, wanda ya ke bajintar gaske ta hanyar bunkasa garkuwar jiki da kuma yakar cututtuka a jikin dan Adam.

KARANTA KUMA: Muna fuskantar kalubale a fagen yaki da cutar covid-19 a Najeriya - NCDC

Gwanda:

Gwanda ta kunshi sunadarai (Vitamin C, Folate, Potassium, B Vitamin) masu tabbatar da bunkasar lafiya a jikin dan Adam da kuma bai wa jiki garkuwa ta yakar cututtuka.

Naman Kaza:

Cin naman kaza bai takaita kadai a wurin motsa kunnuwa ba, domin kuwa har ta kashin kaza yana kunshe da sunadarai masu inganta lafiyar bil Adama.

Kifi mai ƙwanso:

Ire-iren namun ruwa wanda halittar su ta kasance a cikin ƙwanso kamar ƙaguwa da sauransu, su na da albarkar sunadarin zinc. Sunadarin Zinc yana bunkasa lafiya da kuma garkuwar jikin dan Adam.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng