NMA ta sanar da mutuwar Likitan da ya kamu da kwayar COVID-19 a Jihar Legas
Mutum 11 su ka mutu a Najeriya a sakamakon kamuwa da Coronavirus. Daga cikin wadanda su ka mutu har da Likitoci da aka sani da kula da wadanda wannan cuta ta kama.
A cikin makon nan ne aka sake samun labarin wani Malamin asibiti da ya kwanta kama a sanadiyyar cutar COVID-19. Kungiyar Lauyoyin kasar ta bayyana wannan a jiya.
A ranar Laraba, 15 ga watan Afrilu, kungiyar NMA ta reshen jihar Legas ta sanar da mutuwar wani Likita. Likitan ya rasu ne bayan wani maras lafiya ya goga masa COVID-19.
NMA ta reshen Legas ta fito shafinta na Tuwita ta na makokin wannan ‘dan ta da ya rasu. Kungiyar ta yi amfani da wannan dama wajen yi wa na-kusa da marigayin ta’aziyya.
Wannan Likita da aka bayyana sunansa a matsayin Chugbo Emeka ya rasu ne yayin da ake kula da shi a asibitin koyon aiki na jami’ar jihar Legas bayan Coronavirus ta kama sa.
KU KARANTA: Likitocin da su ka zo daga Sin garau su ke inji gwamnatin Najeriya
Jawabin da kungiyar ta fitar ya ce: “Kungiyar NMA ta Legas ta na mai takaicin sanar da mutuwar Dr. Chugbo Emeka a dakin killace marasa lafiya na asibitin koyon aiki na LUTH.”
Kungiyar ta kara da cewa: “Ya mutu ne a ranar 15 ga watan Afrilu, 2020. (Marigayin ya kasance) Likita ne mai zaman kansa wanda ya kamu da cutar daga wani mai COVID-19.”
A karshen jawabi da aka yi a Tuwita, kungiyar Lauyoyin kasar na reshen Legas ta ce: “Mu na yi wa Danginsa da Duniyar Likitoci ta’aziyyar wannan mummunan rashi da aka yi”
Kafin yanzu an samu wani Likita mai suna Aliyu Yakubu wanda COVID-19 ta kashe. Yakubu ya rasu ne a asibitin Sojin sama a Daura bayan ya kamu da cutar a wata tafiya da ya yi.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng