COVID-19: Hotunan yadda dan kamfai na mata ya zama takunkumin rufe fuska a Kenya

COVID-19: Hotunan yadda dan kamfai na mata ya zama takunkumin rufe fuska a Kenya

Wani sashi na mazauna kasar Kenya a Murang sun koma amfani da dan kamfai na mata da aka sarrafa shi ya koma tamkar takunkumin rufe fuska.

Wasu yan kasuwa ne dai suka damfari mutane suka rika sayar musu wannan sabon samfurin takunkumin kamar yadda shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

Da suke magana da Inooro TV, wasu mazauna unguwar sun ce araha ce ta saka suka saya takunkumin rufe fuskan.

Ana sayar musu da takunkumin ne a kan kudi Ksh. 2O kacal ko wane guda inda suka ce sai bayan sun dade da siya ne suka lura cewa dan kamfai na mata suke saka wa.

Covid19: Hotunan yadda dan kamfai ya zama takunkumin rufe fuska a Kenya
Covid19: Hotunan yadda dan kamfai ya zama takunkumin rufe fuska a Kenya
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Shekau ya fadi maganin coronavirus a cikin sabon sakon sautin murya da ya fitar

Mazauna unguwar sun bukaci gwamnati ta samar musu da sabbin takunkumin rufe fuskan sakamakon damuwar da suka shiga na rashin gamsuwa game da ingancin dan kamfan wurin kare su daga kamuwa daga cutar.

Covid19: Hotunan yadda dan kamfai ya zama takunkumin rufe fuska a Kenya
Covid19: Hotunan yadda dan kamfai ya zama takunkumin rufe fuska a Kenya
Asali: Twitter

Hakan na zuwa ne bayan gwamnatin kasar ta umurci dukkan mutane su rika saka takunkumin rufe fuskan a duk lokacin da za su fita waje.

Har wa yau, gwamnatin ta ce za ta rufe duk wani shago ko kanti da aka samu yana sayar wa mutane kaya ba tare da sun rufe fuskokinsu da takunkumin ba.

Covid19: Hotunan yadda dan kamfai ya zama takunkumin rufe fuska a Kenya
Covid19: Hotunan yadda dan kamfai ya zama takunkumin rufe fuska a Kenya
Asali: Twitter

Gwamnatin kasar ta bawa masu ababen sufuri irin wannan umurnin inda ta umurci dukkan yan kasar su rika saka takunkumin fuskar yayin da za su yi tafiye tafiye.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel