Jibril, Nur Husseini da sauran wadanda COVID-19 ta kashe a Afrika

Jibril, Nur Husseini da sauran wadanda COVID-19 ta kashe a Afrika

Daga karshen shekarar 2019 zuwa yanzu, an samu mutane sama da miliyan biyu da su ka kamu da cutar COVID-19 a Duniya, daga ciki an yi dace fiye da 500, 000 sun samu sauki.

Ko da wannan cuta ta hallaka kusan mutum 140, 000 a fadin Duniya, a halin yanzu wadanda su ka mutu a sanadiyyar cutar a nahiyar Afrika ba su yi yawan da aka yi tunani ba.

Duk da haka an samu wadanda cutar ta hallaka a nahiyar. Daily Trust ta kawo wasu daga cikinsu:

1. Mahmud Jibril

Tsohon firayim minista na kasar Libya Mahmoud Jibril ya na cikin wadanda cutar COVID-19 ta kashe. Mahmud Jibril ne ya jagoranci ‘yan tawaye wajen tunbuke gwamnatin Muammar Gaddafi a Libya.

2. Nur Husseini

A Landan ne tsohon firayim ministan kasar Somalia, Nur Husseini ya cika. Husseini wanda ya mulki kasarsa tsakanin 2007 zuwa shekarar 2009 ya mutu ne bayan da cutar Coronavirus ta ci karfinsa.

3. Zororo Makamba

Zororo Makamba fitaccen ‘dan jarida ne wanda Coronavirus ta ga bayan sa. Makamba ya mutu ne a ranar 23 ga watan Maris. Matashin ya cika a babban birnin Zimbabwe watau a Harare ya na da shekaru 30.

KU KARANTA: Za a rika koya karatu a gidajen rediyo da talabijin a lokacin COVID-19

4. Jacques Joaquim Yhombi-Opango

Tsohon shugaban kasar Kongo, Jacques Joaquim Yhombi-Opango ya na cikin jerin wadanda annobar ta ga bayansu a Afrika. Yhombi-Opango ya taba rike firayim minista da shugaban kasa a Kongo.

5. Aurlus Mabele

A cikin watan Maris shararren mawakin nan wanda ake yi wa kirari da sarkin Soukous watau Aurlus Mabele ya cika. Aurélien Miatsonama ya rasu ya na da shekara 67 a sakamakon kamuwa da COVID-19.

6. Manu Dibango

Wani tsohon shararren tauraro da ya mutu a sanadiyyar wannan cuta shi ne Manu Dibango. Dibango wanda ya yi tashe a shekarun baya ya rasu ne a watan jiya yana da shekaru 86 a Duniya.

7. Mohammed Farah

Tsohon ‘dan wasan kasar Somaliya Abdulkadir Mohammed Farah ya yi shahada bayan barkewar annobar Coronavirus. Farah ya na cikin hadiman ministan wasannin Somaliya kafin mutuwarsa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel