Gudumuwa: Kuskure aka samu bankuna su ka biya albashin Maris – Majalisa

Gudumuwa: Kuskure aka samu bankuna su ka biya albashin Maris – Majalisa

Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto cewa ‘yan majalisar wakilan tarayya sun dakatar da batun bada albashinsu a matsayin gudumuwa wajen yakar annobar cutar COVID-19 a Najeriya.

Rahotanni sun tabbatar cewa ‘yan majalisar da su ka yi alkawarin sadaukar da kudinsu sun riga sun fara karbar albashinsu, hakan ya nuna an dakatar da wannan alkawari da aka dauka.

Kwanakin baya shugaban majalisar wakilai watau Femi Gbajabiamila ya bayyana cewa abokan aikinsa za su hakura da albashinsu na watanni biyu domin a yaki Coronavirus a Najeriya.

A wancan lokaci, Gbajabiamila ya bayyana cewa za su fara bada wannan gudumuwa ne daga albashin Watan Maris. Sai dai yanzu rahotanni sun zo mana cewa akasin hakan ne ya faru.

Wasu daga cikin ‘yan majalisar wakilan sun fara karbar albashinsu na watan da ya gabata. Wani ‘dan majalisa da albashinsa su ka shigo hannunsa ya tabbatarwa ‘yan jarida wannan labari.

Haka zalika wannan ‘dan majalisa ya ce tuni wasu daga cikin takwarorinsa su ka samu na su albashin. Jaridar ta fitar da wannan rahoto ne a Ranar Alhamis, 16 ga Watan Afrilu, 2020.

KU KARANTA: Tirsasa mu aka yi mu ba sadaukar da albashinmu - 'Dan Majalisa

Gudumuwa: Kuskure aka samu bankuna su ka biya albashin Maris – Majalisa

‘Yan Majalisa za su bada gudumuwar albashin Afrilu da Mayu wajen yakar COVID-19
Source: Facebook

Wani ‘dan majalisa da ya karbi albashinsa ya fadawa jaridar cewa: “Shugaban majalisa ya ce za mu bada albashin Maris da Afrilu, amma wasu sun fara karbar albashin Maris a jiya.”

Wannan Bawan Alah ya kara da cewa: “Da alamu abubuwa ba su tafiya daidai tsakanin shugabannin majalisa da Akawu wanda ke da alhakin tura kudin zuwa wani asusun”

Hon. Solomon Maren mai wakiltar yankin Filato a majalisar ya shaidawa manema labarai cewa albashinsa sun shigo hannunsa, har ma sai da ya kira Kakakin majalisa ya ji dalili.

“Akawu ya yi wa shugaban majalisa bayanin abin da ya faru, lokacin da aka bada umarnin a zaftare wannan kudi an riga an makara, bankuna sun kammala aikin biyan albashin.”

“Tun da ba za a iya maida kudin ba, yanzu za a fara cire gudumuwar ne a Afrilu da Mayu. Kun san yanzu bankuna ba su aiki.” Benjamin Okezie Kali ya ce kuskuren ba daga gare su ba ne.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Newspaper

Online view pixel