Coronavirus: Jahar Neja ta sallami mutane 27 da aka killace

Coronavirus: Jahar Neja ta sallami mutane 27 da aka killace

Gwamnatin jahar Neja a ranar Laraba, 15 ga watan Afrilu, ta sallami mutane 27 da aka zarga da cutar COVID-19, wadanda aka killace, bayan gwaji ya nuna basa dauke da mummunar cutar.

Kwamishinan lafiya na jahar, Dr Muhammad Makusidi, ne ya bayyana hakan ga manema labarai, a yayin da ake sakin mutanen a cibiyar killace marasa lafiya da ke Minna.

Ya yi bayanin cewa mutanen na daga cikin wadanda suka yi tarayya da mutum na farko da aka zarga da cutar a Makera, karamar hukumar Mashegu, wanda sakamako ya nuna baya da cutar.

Kwamishinan ya bayyana cewar babu amfanin ci gaba da killace su bayan sakamakon gwaji ya nuna basa dauke da cutar, don haka aka sake su domin su koma ga iyalansu.

Ya kara da cewar, an sallami wani da ake zargi da cutar wanda aka dauko a Bay Clinic, bayan sakamakon gwajin ya nuna baya dauke da cutar.

Coronavirus: Jahar Neja ta sallami mutane 27 da aka killace

Coronavirus: Jahar Neja ta sallami mutane 27 da aka killace
Source: Twitter

Ya kuma yi karin haske a kan wata da aka zarga da ccutaar a yankin Stadium Junction Minna, cewa tana kan hanyar wucewa daga Onitsha zuwa jahar Kebbi. Amma an yi mata gwajin zazzabi da sauran muhimman gwaje-gwaje kafin aka bari ta ci gaba da tafiyarta.

Sannan ya ce an sanar da hukumomin da ya kamata a jahar Kebbi.

Ya ce zuwa yanzu dai jahar ta kula da mutane 20 da suka nuna alamun cutar, inda a yanzu mutane bakwai ke a cibiyar killace masu cutar, yayinda aka ba sauran yan tsirarun mutane damar killace kansu a gidajensu.

Kan mutum na farko da aka samu da cutar a jahar, Makusidi ya bayyana cewa yana samun sauki da kulawa a cibiyar killace masu cutar da ke babban asibitin Minna.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Coronavirus: An sake sallamar mutane 3 a Abuja

Ya kuma bukaci jama’a da su yi watsi da duk wani rahoto da ke nuna an sake samun wanda ya kamu, indai ba hukumomin da ya kamata bane suka sanar da hakan.

Ya yi kira ga jama’a da su ci gaba da bin dokoki kamar yadda kwararru a fannin lafiya da gwamnatin jahar suka yi umurni.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel